Hamas za ta saki mahaifin ƙaramin yaron da take garkuwa da shi

Magidanci da matarsa da kuma yaransa

Asalin hoton, Family handout

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Ƙungiyar Hamas ta fitar da sunayen mutane uku da za ta saki gobe Asabar ƙarƙashin yarjejejniyar tsagaita wuta da Isra'ila.

Mutanen su ne Israelis Ofer Kalderon, mai shekara 53, da Yarden Bibas, mai shekara 34, da kuma ɗan Isra'ila asalin Amurka, Keith Siegel, mai shekara 65.

Bibas shi ne mahaifin Kfir, jariri mai wata 10 lokacin da aka yi garkuwa da shi, wanda shi ne mafi ƙanƙanta cikin mutanen da aka yi garkuwa da su.

An kuma yi garkuwa da matarsa, Shiri da wani ɗan nasu Ariel mai shekara huɗu.

Ofishin firaministan Isra'ila ya tabbatar da samun jerin sunayen mutanen da za a saki goben.

Ita ma a nata ɓangare, Isra'ila za ta saki wasu rukunin Falasɗinawa da ke tsare a gidajen yarinta.

Sakin nasu zai zama na huɗu tun bayan fara musayar fursunonin da aka fara bayan fara aiki da yarjejeniyar tsagaita wutar da ta fara aiki ranar 19 ga watan Janairu.

Ƙungiyar Hamas ta yi garkuwa da mutum 251 bayan harin ranar 7 ga watan Oktoban 2023 tare da kashe mutum1,200 a harin da kungiyar ta kai cikin Isra'ila.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Harin ya kuma janyo mummunan yaƙin da ya ɗaiɗaita Gaza.

Hare-hare sojojin Isra'ila na tsawon wata 15 ya kashe Falasɗinawa 47,460 a yankin Gaza, a cewar ma'aikatar lafiyar Hamas da ke Gaza.

Hamas ta yi garkuwa da Ofer Kalderon da Yarden Bibas daga Nir Oz, yayin da suka kama Keith Siegel a Kfar Aza.

Sannan kuma aka kama matar Bibas, Shiri tare da 'ya'yansu biyu, waɗanda har yanzu ba a san halin da suke ciki ba.

Sakin mutanen uku zai sa adadin mutanen da Hamas ya ƙaru zuwa 18.

Ƙungiyar fursunonin Isra'ila ta ce mutum tara daga cikin waɗanda za a saki gobe na zaman hukuncin ɗaurin rai da rai ne, yayin da 81 ke zaman dogon lokaci a gidajen yarin Isra'ilar.

To sai dai a nata ɓangare Isra'ila ba ta ce komai ba game da Falasɗinawan da za ta saki.

Kawo yanzu an saki Falasɗinawa 400 - kama daga waɗanda ke zaman dogon lokaci saboda laifukan tayar da bama-bamai zuwa matasan da ake tsare da su ba tare da wata tuhuma ba.

Da dama an mayar da su Gaɓar Yamma da Kogin Jordan da gabashin Birnin Kudus da kuma yankin Gaza, yayin da aka fitar da masu manyan laifuka zuwa ƙasashen waje.

Isra'ilawan da aka saki jiya Alhamis ya bayyana rashin tsari a sakin mutanen, lamarin da bai yi wa Isra'ila daɗi ba har ta kai ga ta jinkirta sakin Falasɗinawa fursunonin da ke hannunta.

Yayin da aka saki mutum bakwai cikin takwas a Khan Younis, dandazon mutanen da suka riƙa kokawar ɗaukar hotuna da wayoyinsu tare da mutanen da aka sakin a lokacin da mayaƙan Hamas ɗin ke tafiya da su zuwa motocin ƙungiyar Red Cross ya haifar da cunkoso.

Ita kuma ɗayar da aka saki a Jabaliya, Hamas ta gabatar da ita a wani gini da sojojin Isra'ila suka ruguza wani ɓangarensa kafin su miƙa ta ga ƙungiyar Red Cross.

To sai dai daga baya ofishin firaministan Isra'ila ya ce ya samu bayani daga masu shiga tsakani cewa ''za a tabbatar da kariya wajen miƙa mutanen da za a saki a nan gaba".