Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kocin Chelsea ya ƙalubalanci kyaftin ɗinsa
Kocin Chelsea Enzo Maresca ya buƙaci “jagoranci na gari” daga kyaftin ɗin ƙungiyar Reece James bayan dawowarsa daga jinya.
Ɗan wasan baya na gefen dama ya murmure daga tiyatar da ya yi a ƙafarsa inda ya buga wasan farko tun watan Disambar 2023 a wasan da Liverpool ta doke Chelsea da ci 2-1 a ranar Lahadin da ta gabata, amma Maresca ya ƙalubalanci kocin nasa da ya nuna halin jajircewa.
"Na yi magana da shi kuma ina sa ran cewa zai nuna shugabanci a tawagar ƴan wasan," in ji Maresca.
Ya ƙara da cewa "Yana matuƙar ƙoƙari, kuma yana samun ci gaba amma ina sa ran zai ƙara ƙaimi fiye da haka.''
James, mai shekaru 24, ya samu ci gaba daga tawagar matasan Chelsea zuwa ƙungiyar farko kuma wanda Maresca ya gada, Mauricio Pochettino ya naɗa shi kyaftin kafin kakar wasa ta 2023-24.
Ɗan wasan bayan na Ingila ya samu cikas sakamakon rauni a kakar wasan da ta gabata, inda ya buga wasanni 11, kafin ya koma taka leda a Anfield a wasansa na farko da ya fafata a ƙarƙashin jagorancin Maresca, wanda ya maye gurbin Pochettino a bazara.
Maresca ya ƙara da cewa "Yana fahimtar abubuwan da mu ke buƙata daga gare shi."