Waiwaye: Harin Boko Haram ga sojojin Najeriya a Marte da fara jigilar maniyyatan ƙasar na bana

Asalin hoton, Getty Images
An shiga makon ne da rahotanni daga yankin arewa maso gabashin Najeriya na mayaƙan Boko Haram sun kai wa sojoji hari a sansaninsu da ke Marte na jihar Borno, inda ake zargin sun kashe wasu sojoji, sannan suka yi awon gaba da wasu.
Bayanan sun ƙara da cewa mayaƙan sun kai harin ne a kan sansani sojojin bataliya ta 153 da tsakar daren wayewar garin ranar Litinin.
Ƴan Boko Haram ɗin sun kai harin ne a kan babura riƙe da makamai, inda suka lallaba sansanin sojin da misalin ƙarfe 3 na dare, kamar yadda bayanai suka nuna.
Za mu koma aikin haƙo ɗanyen mai a arewacin Najeriya - NNPCL

Asalin hoton, NNPC Limited/Facebook
Haka kuma a farkon ne abon shugaban kamfanin man fetur na Najeriya Bayo Ojulari ya faɗa wa BBC cewa za a koma aikin haƙo ɗanyen man fetur a arewacin Najeriya bayan shekara biyu da ƙaddamar da aikin haƙowa a iyakar jihohin Bauchi da Gombe - wanda tun daga wancan lokaci ba a ci gaba da aikin ba.
Aikin da aka ƙaddamar a gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari da ta gabata, ya sanya al'ummar arewacin ƙasar sun fara kyakkyawar fatan cewa yankin zai bi sahun wasu yankunan ƙasar da ke samar da man fetur wanda tattalin arzikin ƙasar ya dogara a kai.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ƴan Najeriya suke cigaba da kokawa kan tsadar rayuwa, wadda ke da alaƙa tashin farashin man fetur a sanadiyar cire tallafin da gwamnati ke bayarwa a bangaren.
Fara jigilar maniyyatan Najeriya na bana

Asalin hoton, NAHCON/X
A ranar Juma'ar makon ne wato 9 ga watan Mayu ne alhazan Najeriya suka fara tashi zuwa ƙasa mai tsarki kamar yadda hukumar alhazan ƙasar ta tabbatar.
Aikin hajji na ɗaya daga cikin rukunai biyar na ginshiƙan imani a addinin Musulunci, duk da dai cewa aikin hajjin na wajaba ne ga mai hali ta fuskar wadata da lafiya.
Ga wasu abubuwa guda biyar da suka kamata ku sani kan aikin hajjin na bana.
Me ya sa ake tababa kan alƙaluman haɓakar tattalin arziƙin Najeriya?

Asalin hoton, Getty Images
A makon ne kuma Bankin Duniya ya fitar da ƙididdigar da ke nuna cewa tattalin arzikin Najeriya na samun tagomashi, lamarin da wasu ƴan ƙasar suka kwatantawa da al'amara.
A wani rahoto da Bankin Duniya ya fitar, tattalin arzikin Najeriya ya samu cigaba a 2024, fiye da kusan shekara 10.
Waɗannan alƙaluman sun fito ne a daidai lokacin da mutanen Najeriya musamman ma'aikata da masu ƙananan sana'o'i suke ƙorafin taɓarɓarewar tattalin arzikinsu, musamman wajen ɗaukar ɗawainiyar iyali da harkokin yau da kullum.
Wane tasiri haramcin fitar da dabbobi daga Nijar zai yi a Najeriya?

Asalin hoton, Getty Images
Masu shirin gudanar da ibadar layya musamman a Najeriya sun fara bayyana fargabarsu kan tashin farashin dabbobin layya, sakamakon matakin da gwamnatin Nijar ta ɗauka na hana fitar da dabbobin zuwa ƙasashen waje.
A makon da ya gabata ne gwamnatin ƙasar ta Nijar ta bayyana matakin haramta fitar da dabbobi zuwa ƙasashen waje.
Cikin sanarwar haramcin da ministan ƙasar, Abdoulaye Seydou ya bayyana, ya ce gwamnatin ƙasar ta ɗauki matakin ne domin tabbatar da samar da wadatuwarsu a kasuwannin ƙasar a wani mataki na karya farashin dabbobin gabanin bukukuwan Sallar Layya.
Me ya rage wa Simon Ekpa, jagoran IPOB da ake tuhuma da ta'addanci a Finland?

Asalin hoton, Simon Ekpa/X
Masu gabatar da ƙara a ƙasar Finland sun gabatar da jagoran IPOB, Simon Ekpa bisa zarginsa da yaɗa ta'addanci ta intanet.
A wata sanarwa da hukumar gabatar da ƙara ta Finland ta fitar, ta ce suna tuhumarsa "bisa ingiza mutane su aikata ɓarna da manufar ta'addanci da kuma shiga cikin ayyukan ƙungiyar ta'adddanci."
Sanarwar ta ce hukumomin ƙasar na zargin Ekpa ne da aikata laifukan a tsakanin shekarar 2021 zuwa 2024. Sun ce tuhumar na da alaƙa da yunƙurin wanda ake zargin na kafa ƙasar Biafra.











