Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Hakim Ziyech ya koma Al-Duhail ta Qatar
Hakim Ziyech ya koma Al-Duhail, kamar yadda ƙungiyar Qatar ta sanar ranar Alhamis, bayan da kwantiragin ɗan kasar Morocco ya kare da Galatasaray.
Mai shekara 31- wanda ya buga wa tawagar Netherlands tamaula ta matasa, zai taka leda karkashin tsohon kociyan Paris Saint-Germain, Christophe Galtier.
"Al-Duhail Sports Club ta yi nasarar rattaba yarjejeniyar ɗaukar ɗan ƙwallon tawagar Moroccan, Hakim Ziyech," kamar yadda Al-Duhail ta sanar.
Ziyech ya buga wasannin aro a Galatasaray daga Chelsea a Agustan 2023 daga nan ƙungiyar Turkiya ta mallake shi a karshen kakar.
Ya lashe Champions League da FIFA Club World Cup tare da Chelsea mai buga Premier League.
Ya kuma taka rawar gani da Morocco ta kai daf da karshe a kofin duniya a 2022 a Qatar, gasar da Argentina ta lashe.