Yamal na cikin ƴan Barca 28 da za su je Saudi Arabia Spanish Super Cup

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Kociyan Barcelona, Hansi Flick ya bayyana ƴan wasa 28 da za su buga wa ƙungiyar Spanish Super Cup a Saudi Arabia a bana, ciki har da Lamine Yamal.

Har yanzu Yamal bai murmure ba daga raunin da ya ji tun daga ranar 15 ga watan Disamba a karawa da Leganes, wanda a lokacin aka ce zai ji jinyar mako uku zuwa huɗu.

Ɗan wasan tawagar Sifaniya bai yi wa Barcelona wasa ba da Atletico Madrid da kuma Barbastro, amma ana sa ran zai warke kafin wasan na Spanish Super Cup.

Barcelona mai fatan lashe kofin farko a 2025, za ta fafata da Athletic Club a wasan daf da karshe a Spanish Super a Saudi Arabia.

Ranar Asabar Barcelona ta kai zagayen ƙungiyoyi 16 a Copa del Rey, bayan da ya doke Barbastro 4-0.

Barcelona tana mataki na uku a teburin La Liga, biye da Atletico Madrid ta biyu da kuma Real Madrid mai jan ragama.

Ƴan wasan Barcelona 28 da za su buga Spanish Super Cup:

Cubarsí, ⁠Balde, R. Araujo, I. Martinez, ⁠Gavi, Ferran, Pedri, ⁠Lewandowski, ⁠Ansu Fati, Raphinha, Iñaki Peña, ⁠Pablo Torre, Christensen da kuma Fermín.

Sauran sun haɗa da M. Casadó, Pau Víctor, Lamine Yamal, Olmo, ⁠F. De Jong, Kounde, Eric, Szczęsny, ⁠Astralaga, Bernal, H. Fort, ⁠Gerard Martín, ⁠S. Domínguez da kuma A. Fernández.