Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ruben Dias na Man City zai yi jinyar makonni
- Marubuci, Simon Stone
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Chief football news reporter
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 1
Manchester City ta sake fuskantar matsala bayan koci Pep Guardiola ya tabbatar ɗanwasan baya na Portugal Ruben Dias zai yi jinyar mako "uku zuwa huɗu".
Dias wanda ya ji rauni a wasan da Manchester United ta cinye su, ba zai buga duka wasannin ƙarshen shekara ba.
Ɗanwasan mai shekara 27 zai yi hanƙoron ganin ya murmure saboda karawarsu da PSG mai muhimmancin gaske a gasar zakarun Turai ta Champions League ranar 22 ga watan Janairu.
Da ma Dias bai buga wasa bakwai ba saboda rauni a cinyarsa a wannan kakar, abin da ya ƙara jefa City cikin matsalar rashin John Stones, da Nathan Ake, da Manuel Akanji, da Kyle Walker waɗanda duka suka ji raunuka a lokuta daban-daban.
A gefe guda kuma gwarzon ɗan ƙwallon Ballon d'Or ba zai sake buga wasa a kakar bana ba saboda raunin da ya ji a gwiwarsa.
"Matsalar a tsoka ne kuma ba zai yi wasa ba tsawon mako uku ko huɗu," in ji Guardiola.
"Bayan minti 75 a wasan United ya ji 'yar matsala. Amma yana da ƙoƙari sosai kuma ya so ya ci gaba da wasan. Yanzu dai ya ji rauni."
Guardiola ya kuma tabbatar cewa Stones, da Akanji, da Mateo Kovacic sun yi atasaye a makon nan kuma za su iya buga wasa da Aston Villa ranar Asabar, amma ya ce Ederson "da wuya" ya iya bugawa.
Yayin da City ta ci wasa ɗaya cikin 11 da ta buga, an yi mamakin yadda Guardiola ya yi amfani da matasan 'yanwasan James McAtee da Nico O'Reilly.