Matar Havertz ta samu saƙonnin cin zarafi a kafar sada zumunta

Kai Havertz

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Matar Kai Havertz ta sanar da samun saƙonnin cin mutunti da zarafi a kafar sada zumunta, bayan tashi wasan da Manchester United ta fitar da Arsenal a FA Cup ranar Lahadi.

Ta kuma ce cikin saƙonnin da ta samu har da na barazana da aka yi musu da ɗan cikin da ko haifarsa ba a yi ba.

Havertz mai shekara 25, ya barar da damar makin da ya kamata ya ci ƙwallayen da zai kai Arsenal zagayen gaba a FA Cup, amma ya yi ta barar da ƙwallaye.

Bayan da suka tashi 1-1 har da karin lokacin, sai aka je bugun fenariti, inda mai tsare ragar United, Altay Bayindir ya tare wadda Havertz ya buga.

Hakan ne ya sa United ta kai zagaye na huɗu a FA Cup da cin 5-3 a bugun daga kai sai mai tsaron raga - za kuma ta fuskanci Leicester City cikin wwatan Fabrairu.

Matar ɗan wasan ɗan kasar Jamus, ta saka cin zarafin da aka yi mata karo biyu a Instagram, daga wanda ta samu a kafar sada zumuntar.

Tuni Arsenal ta shigar da korafi ga ƴansanda, waɗanda suka shiga aiki don zakulo waɗanda suka aikata laifin.

BBC ta tuntuɓi jami'an tsaro domin karin bayanai.

Havertz yana tare da mai ɗakinsa tun daga 2018, inda ya auri Sophia, wadda a bara ta sanar a cikin watan Nuwamba cewar tana ɗauke da juna biyu.