Mata ya koma WSW kan kwantaragin shekara guda

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Tsohon ɗan wasan Manchester United da Chelsea Juan Mata ya koma ƙungiyar Western Sydney Wanderers ta Lig A kan kwantaragin shekara daya.

Dan spaniyan mai shekara 36 ya dade ba shida ƙungiya tun bayan barin Vissel Kobe ta Japan a farkon watan Janairun 2024.

Mata ya bar Ingila ne a 2022 ya koma Galatasary, inda ya lashe kofin ƙasar a shekara ɗayan da ya yi a Turkiyya.

"Ina cikin farin cikin komowa Western Sydney Wanderers, ƙungiyar Australia ɗaya tilo da ta taɓa lashe Asian Champions, ji nake kawai lokaci yazo na tafi na fara atisaye da abokan wasana," in ji Mata.

"Ina cikin godiya da farin ciki kan sabon yanayin da zan samu, kuma ina fatan zan sake lashe Champions da wata ƙungiyar ta daban."

Mata ya bugawa Spainiya wasanni 40, ya kuma koma Chelsea ne a shekarar 2011 daga Valancia kan kuɗi fan miliyan 23.5.

Dan wasan ya taka leda sosai a Stamford Bridge yadda ya kamata, inda ya lashe ɗan wasan mafi kwazo a shekara sau biyu a shekara biyun da ya yi a ƙungiyar West London.

Mata ya lashe Champions Lig da FA a Chelsea a 2012, da kuma Europa Lig a 2013.

Dan wasan tsakiyar na cikin tawagar Spaniya da ta lashe Kofin Duniya a 2010 suka kuma lashe Euro 2012.

Ya koma Manchester United a 2014 a matsayin ɗan wasa mafi tsada inda ya kwashe shekara takwas a Old Trafford.

Mata ya ci kwallo a wasan da United ta dole Crystal Palace a wasan ƙarshe na FA a 2016, sannan ta lashe EFL da kuma Europa 2017.

A 2022 ya bar ƙungiyar bayan ƙarewar kwataraginsa ya kuma koma Galatasaray. Ya ci kwallo 51 a wasa 285 da ya buga wa ƙungiyar ta Old Trafford.