Leicester za ta karɓi bakuncin Tottenham a King Power

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Leicester City za ta karɓi baƙuncin Tottenham a wasan makon farko a Premier League ranar Litinin a King Power.

Sai dai Leicester za ta buga wasan ba tare da Jamie Vardy da Patson Daka ba, waɗanda ke jinya in ji Steve Cooper.

Shima mai tsaron bayan ƙungiyar, Conor Coady na jinya.

Ɗan wasan Tottenham, Yves Bissouma ba zai yi wasan ba, bayan da ƙungiyar ta dakatar da shi.

Ana sa ran sabon ɗan ƙwallon da ta ɗauka daga Bournemouth a bana, Dominic Solanke zai fara wasan farko a Tottenham, bayan da har yanzu Richarlison ke jinya.

Wasa tsakanin ƙungiyoyin biyu

An ci ƙwallo 128 a karawa 34 a Premier League tsakaninsu. Shi ne wasan da aka fi zazzaga ƙwallaye a raga a haɗuwa sama da 20 a gasar.

Rabon da su fuskanci juna tun 2022/23, inda Tottenham ta ci 6-2, ita kuma Leicester ta yi nasara 4-1 a King Power.

Leicester City

Wasa biyar baya da Leicester ta yi a ranar buɗe labulen gasar ba ta yi rashin nasara ba, wadda ta ci uku da canjaras biyu.

Sai dai a karawa biyar Leicester ba ta yi nasara ba a fafatawar ranar Litinin tun bayan 4-0 da ta doke Nottingham Forest a lokacin Steve Cooper.

Wasan karshe da Cooper ya ja ragama a Premier League shi ne wanda Tottenham ta doke Nottingham Forest 2-0 a Disambar bara.

Tottenham

Wasa ɗaya ne Tottenham ta yi rashin nasara daga takwas a ranar buɗe labulen Premier League, shi ne wanda Everton ta ci 1-0, Tottenham ta ci biyar da canjaras biyu daga ciki.

Ƙungiyar da Ange Postecoglou ke jan ragama da Arsenal da Manchester City sun hada maki uku a sabbin ƙungiyoyin da suka buga kakar bara.

Son Heung-min ya ci Leicester City ƙwallo tara da bayar da huɗu aka zura a raga a wasa 14 da ya fuskanci ƙungiyar.

Idan Dominic Solanke ya ci ƙwallo zai zama na farko a wasan farko da ya yi wannan bajintar, bayan Steven Bergwijn a karawar da Tottenham ta doke Manchester City 2-0 a 2020.