Matashiya mai aikin birkila da mata ƴanuwanta ke tsangwama

Bayanan bidiyo, Latsa alamar da ke sama domin kallon matashiyar mai aikin birkila
Matashiya mai aikin birkila da mata ƴanuwanta ke tsangwama
An wallafa

Wata matashiya da ke sana'ar birkila a jihar Gombe ta ce ta fi fuskantar tsangwama daga takwarorinta mata, idan sun hange ta tana kwaɓa sumunti da jera bulo a wurin aikinta na gini.

Dorcas Mu'azu ta ce ta shiga aikin gini ne wanda maza suka yi kaka-gida musamman a wannan yanki, saboda ta samu halaliya kuma ta hanya mai tsafta domin ta taimaki iyaye da ƙannenta.

Ta ce tana alfaharin cewa tana cikin maginan da suke gina gidaje da masu bene, kai har gidan mai an gina da ita a yankin.

Matashiyar 'yar shekara 22 ta ce ko da yake birkilanci, aiki ne mai wahala da buƙatar ƙarfi da juriya amma ya fiye mata kuma iyayenta suna alfahari da ita.

Ta ce a lokuta da yawa wasu mazan sukan ƙarfafa mata gwiwa ta hanyar yaba mata da yi mata kyauta.

Dorcas ta ce tana da burin ta ci gaba da karatu zuwa kwaleji ko jami'a a duk lokacin da ta samu hali.