Real Madrid za ta je Las Palmas buga La Liga ranar Alhamis

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Real Madrid za ta je gidan Las Palmas ranar Alhamis, domin buga wasan mako na uku a La Liga da za su fafata a Gran Canaria.

Real Madrid tana da maki huɗu a wasa biyu a gasar bana, bayan da ta fara yin 1-1 a gidan Real Mallorca da cin Real Valladolid 3-0 ranar Lahadi.

Ita kuwa Las Palmas maki ɗaya take da shi, bayan da ta fara yin 2-2 a gida da Sevilla, sannan Leganes ta doke ta 2-1.

Ƙungiyoyin biyun sun kara a bara, inda Real Madrid ta ci 2-0 a Santiago Bernabeu ranar Laraba 27 ga watan Satumbar 2023.

A wasa na biyu a La Liga da suka fafata ranar Asabar 27 ga watan Janairun 2024, inda Las Palmas ta yi rashin nasara 2-1 a gida.

Watakila a wasan na ranar Alhamis, sabon ɗan ƙwallon da Real Madrid ta ɗauka a bana daga Paris St Germain, Kylian Mbappe ya fara ci mata ƙwallo a gasar.

Ƙyaftin ɗin Faransa, wanda shi ne ya ci ƙwallo na biyu a Uefa Super Cup da Real Madrid ta doke Atalanta 2-0 a watan nan, bai zura ƙwallo a raga ba a wasa biyun da ta yi a La Liga.

Tuni Carlo Alcelotti ya bayyana ƴan wasan da ya je da su Las Palmas a karawar ta mako na uku a babbar gasar tamaula ta Sifaniya.

Ƴan wasan Real Madrid;

Masu tsaron raga: Courtois, Lunin da kuma Fran González.

Masu tsaron baya: Carvajal, Militão, Lucas V., Fran García, Rüdiger, Mendy da kuma Jacobo.

Masu buga tsakiya: Valverde, Modrić, Tchouameni, Arda Güler da kuma Ceballos.

Masu cin ƙwallaye: Vini Jr, Mbappé, Rodrygo, Endrick da kuma Brahim.