Chelsea ta karɓi Felix daga Atletico ta bayar da Gallagher

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Chelsea ta ƙulla yarjejeniya da Atletico Madrid, inda ta ɗauki Joao Felix, ita kuma ta bayar da Conor Gallagher.

Sai dai ba a fayyace ƙudin da ta ɗauki ɗan ƙwallon tawagar Portugal mai shekara 24 ba, amma zai sake komawa Stamford Bridge kan yarjejeniyar kaka biyar.

Haka kuma Chelsea ta ce za ta iya kara tsawaita zaman Felix kaka daya a ƙungiyar da zarar ya taka rawar gani.

Felix, wanda zai je a auna koshin lafiyarsa a Ingila, zai buga tamaula a Chelsea karo na biyu, bayan wasannin aro da ya yi mata a 2023.

Ya ci ƙwallo huɗu a wasa 20 da ya buga wa ƙungiyar Stamford Bridge.

Shi kuwa ɗan wasan tawagar Ingila, Gallagher zai saka hannu kan yarjejeniyar kaka biyar a ƙungiyar da ke buga La Liga.

Chelsea ta hakura da sayen Samu Omorodian, hakan ya sa aka samu tsaikon ɗaukar Gallagher kan £33m, bayan da Atletico ta sayi Julian Alvarez daga Manchester City.

Haka kuma Chelsea na fatan sayen Victor Osimhen daga Napoli kafin a rufe kasuwar cinikin ƴan kwallo ta Turai ta bana ranar 30 ga watan Agusta.

Ita kuwa Napoli na son ɗaukar aron Romelu Lukaku da cewar za ta saye shi daga baya kan £25.5m.

To sai dai da ƙyar ne idan Chelsea za ta amince da farashin, wadda take cewar darajar ɗan ƙwallon tawagar Belgium ta kai £35m.