Yadda safarar bindigogi daga Amurka ta ɗaiɗaita Haiti

- Marubuci, Jacqui Wakefield, Christopher Giles and Joshua Cheetham
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Global Disinformation Unit, BBC World Service
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 7
Ɗaruruwan harsasai da bindigogi sun isa Haiti cikin wasu akwatuna biyu, an saka akwatunan cikin kayan abinci da tufafi da aka kai ƙasar - cikin wani jirgin ruwan daƙon ƙaya.
Sun fito ne daga Amurka, wanda wani ƙwararre ya kwatanta a matsayin "babban kasuwa" da ke tura wa gungun ƴan daba makamai da suka janyo ruɗani da tashin hankali a ƙasar.
Wani bincike da BBC ta gudanar tare da bin diddigin akwatunan guda biyu, domin gano yadda makamai suka isa Haiti daga Amurka. An gano rashin bin dokoki da yin bincike a hanya da kuma zargin ba da na nagoro da masu fasa kwauri ke yi don wuce shingen dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Ɗinkin Duniya.
Ƙwace akwatuna
Rundunar ƴan sandan ƙasar Haiti ta sanar a watan Afrilun 2024 cewa ta ƙwace akwatunan biyu. Suna ɗauke da manyan bindigogi 12, da ƙananan bindiga ƙirar pistol 14 da kuma harsasai 999.
Wani hoto da ƴansanda suka ɗauka ya nuna makaman waɗanda wasu kamfanonin Amurka biyu suka ƙera.
An yi tafiyar kusan kilomita 1,200 daga garin Fort Lauderdale a jihar Florida zuwa Cap-Haitien a arewacin Haiti domin kai makaman.

Asalin hoton, Ƴan sandan Haiti
An ajiye kwantenar da aka saka makaman a gidan ajiya a birnin Fort Lauderdale, a cewar wasu ƙwararru a Amurka, waɗanda aka ɗora wa alhakin saka ido kan takunkuma da aka saka wa Haiti, da kuma suka yi bincike kan aika makaman.
Ƴan Haiti da ke zaune Amurka sun sha aika abinci da sauran kayayyaki da ake buƙata zuwa ƙasar.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Wani mutum mai suna Anestin Predestin ya faɗa wa jaridar Miami Herald cewa a watan Fabrairun 2024 cewa ya samu gurbi a cikin kwantenan domin aika kaya.
Ya faɗa wa jaridar cewa wani mutum da ya ce sunansa "Diamortino" ya saka akwatuna biyu inda ya ce suna ɗauke da "tufafi" - kuma ya kaɗu da ya gano cewa suna ɗauke da makamai.
Ƙoƙarin da BBC ta yi wajen ji daga Mista Predestin ya citura.
Ba a dai san daga wajen da aka sayi bindigogin ba. Ba a ƙera bindigogi a Haiti, kuma ƙwacen da aka yi a baya ya kunshi bindigogi da aka saya daga Florida.
Florida wadda ake wa laƙabi da "jihar bindigogi", ta kasance ɗaya daga cikin jihohi 30 da mutanen da ba su da rajista ke sayar da makamai har sai zuwa 2024, Alal misali a bayyane da kuma kan yanar gizo, ba tare da an yi ƙwaƙƙwarar bincike ba. A lokacin mulkinsa, Joe Biden ya tsaurara matakai kan haka a faɗin ƙasar.
Tawagar Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce wasu ƴan Haiti biyu da suka kasance ƴan uwa waɗanda ke zaune a Amurka, sun riƙa amfani da wasu mutane a maimakonsu - wajen sayan makamai tare da aika su Haiti.
Ƙwararru sun ce wannan ba sabuwar hanya ba ce, inda a yawan lokuta ake tura bindigogi zuwa ƙasar ta hanyar yin dabaru.
Aika makamai
Wani kamfani mazaunin Florida da ke hada-hadar aika kayayyaki ne, ya tura kwantenan da ke ɗauke da makaman zuwa Haiti.
Kamfanin ba shi da jiragen ruwan daƙon kaya da ke tafiya zuwa Haiti, amma yana sayen gurbi a cikin jiragen sannan ya sayarwa wasu mutane kamar Mista Predestin.
Shugaban kamfanin, Gregory Moraille, ya bayyana cikin wata sanarwa da ya aika wa BBC cewa, suna samar da kwantenoni da ba su ɗauke da komai ga kwastomomi, sai dai ba su yin magana da masu tuka jiragen.
"Abin takaici, ba mu da takamaimen hanyar hana aika makamai," in ji shi, inda ya ƙara da cewa kamfanin na bai wa hukumomi haɗin-kai kuma yana da ma'aikata da dama da suka fito daga Haiti.
"Abin damuwa, ƴan uwan mu da dama sun faɗa cikin wannan rikici da ake fama da shi a Haiti," in ji shi.
Fitar jirgin ruwan daƙon ƙaya daga Amurka
BBC ta tuntuɓi hukumar kwastam ta Amurka da kuma jami'an kula da iyakoki domin sanin cewa ko an binciki jirgin da ya ɗauki makaman kafin ya bar Amurka, amma babu wani martani.
Tawagar ta MDD ta ce a watan Satumbar da ta gabata Amurka ta ƙara ƙaimi wajen bincike, sai dai "ba a binciken kwantenoni kusan 200 da ke fita daga Florida zuwa Haiti a kowane mako".
Wani tsohon jami'i a hukumar takaita yaɗuwar makamai da kula da ganyayyakin taba na tobacco da kuma abubuwan fashewa ta Amurka, Bill Kulman, ya shaida wa BBC cewa "ba a cika yin binciken da ya kamata ba kan jiragen dakon kaya da ke fita, kuma suna da yawan gaske.
Isa zuwa Haiti
Ƴan sandan Haiti sun ce sun gano makaman ne a "wani bincike" da suka gudanar a cikin kwantenar da ke ɗauke da jirgin ya ɗauka.
A cewar tawagar ta MDD, wani babban jami'in kwastam a Haiti ya saka ɗaya daga cikin akwatunan da ke ɗauke da makaman cikin motarsa, kuma an kama shi tare da sallamarsa daga aiki kwanaki kaɗan bayan faruwar lamarin.
Jami'an ƴan sandan sun ce suna neman wani mutum mai suna Wilmane Jean, wanda yake cikin kundin hukumar kwastam a ƙasar - a matsayin mutumin da ya amshi kayayyakin.
BBC ta gano cewa ya kasance wanda ke taimaka wa mutane wajen shiga da fitar da kayayyaki, kuma ya tsere inda ake zarginsa da alaƙa da ƴan daba da suka addabi arewacin ƙasar.
Wani rahoton Majalisar Ɗinkin Duniya a baya, ya ce jami'an kwastam a Haiti suna fama da rashin yawan jamai'ai, cin hanci tsakanin manyan jami'ai da kuma barazanar hare-hare daga gungun ƴan daba.
BBC ta yi ƙoƙarin tuntuɓar hukumomin kwastam a Haiti don ji daga gare su, amma lamarin ya citura.
Ƙarfin gungun ƴan daba
A lokacin da aka kai makaman zuwa Haiti, ana fama da tashin hankali sakamakon ayyukan gungun ƴan daba a Port-au-Prince, babban birnin ƙasar.
Ƴan daba sun saki dubban fursunoni daga babban gidan yarin ƙasar, da kuma toshe tashar jiragen ruwan ƙasar da kuma filayen jirgin sama.
A watan Maris ɗin 2024, Firaiminista Ariel Henry, da ya ƙasa komawa gida daga wata ziyara da ya kai waje, ya amince ya yi murabus.
An kashe mutum 5,601 sakamakon rikicin ƴan daba a Haiti a 2024, a cewar MDD. Ta ce kusan kashi goma na al'ummar ƙasar - mutum kusan miliyan ɗaya - sun tsere daga ƙasar kuma rabinsu na fama da yunwa.
Ayyukan garkuwa da mutane da kuma tilasta karɓar kuɗi a hannun mutane na ƙaruwa a ƙasar.

An harbi Wilson, wani mai sana'ar hannu a Port-au-Prince a kafa, yayin da yake ƙoƙarin tserewa a lokacin da ƴan daba ke artabu don iko da wani yanki a makwabtansa.
"Abin ruɗani ne matuka, kowa na tserewa daga gidansa," ya faɗa wa BBC. "Kafata ta daina aiki. Lokacin da na kalli kasa, jini ne yake ta zuba."
A yanzu yana rayuwa ne a wata makarantar da aka mayar tanti tare da ɗaruruwan mutane.
Ƙwararru sun ce hukumomi ba su da ƙarfin sake karɓe iko, duk da irin taimakon da suke samu daga wata rundunar tsaro ta ƙasa da ƙasa ciki har da aƙalla ƴan sanda 800 daga Kenya.
Ƴan dabar sun ƙwace yankuna da dama a watanni shida da suka wuce, kuma yanzu suna iko da aƙalla kashi 85 na babban birnin ƙasar, a cewar Romain le Cour, wani ƙwararre a wata cibiyar daƙile ta'addanci da ke da hedkwata a Geneva.
Wasu daga cikin ƴan dabar na wallafa hotunansu a kafofin sada zumunta a wasu lokuta riƙe da manyan makamai. Ƙwararru sun faɗa wa BBC cewa wasu daga cikin makaman da ke hannun ƴan dabar an ƙera su a Amurka.
Sai dai, ana ci gaba da kai makamai ƙasar", a cewar Mista Le Cour, wanda shi ne silar tashin hankali da kuma rashin zaman lafiya da Haiti ke fama da shi.
Aika ɗaruruwan kayayyaki
Domin yin bincike kan irin girma safarar makamai daga Amurka zuwa Haiti, BBC ta yi duba kan alkaluman hukumar kwastam ɗin ƙasar ta wallafa kuma uka gani.
Mun haɗa jerin mutanen da aka saka wa takunkumi kan zargin alaƙa da ƴan daba a Haiti, da kuma saura waɗanda aka kama a Haiti ko Amurka a matsayin waɗanda ake zargi da safarar makamai.
Mun duba waɗannan sunaye tare da dubban alkaluman kayayyaki da aka aika daga Amurka zuwa Haiti cikin shekara huɗu.
A jimilla, mutum 26 da ke cikin jerin an bayyana su a matsayin waɗanda suka karɓi kayayyakin da aka tura da suka kai 286, wanda ya faru kafin a saka wa mutanen takunkumi ko kama su. Babu tabbacin cewa ko waɗannan kayayyaki na ɗauke da makamai ba.
An bayyana sunan Prophane Victor har sau 24 a matsayin wanda yake karɓan wasu daga cikin kayayyakin da ake kai wa Haiti - ya kasance tsohon jami'in majalisar dokokin Haiti wanda daga baya MDD da Amurka suka saka wa takunkumi saboda bai wa ƴan daba makamai da kuma safarar makamai. An kama shi a Haiti a watan Janairu.
Shin za a iya dakatar da masu safarar?
"Da farko, hukumomin Amurka ba su yin abin da ya kamata," in ji Mista Le Cour.
Mista Kullman, tsohon jami'in Amurka, ya ce babu wata doka da ta ce masu sayar da bindiga su kai rahoton waɗanda ke saya da ba su yarda da su ba.
Da wuya a samu sauye-sauyen dokoki kan amfani da bindiga a Amurka yanda ya kamata", in ji shi, amma ya ce yana son ganin an yi wani abu kan masu sayar da makamai da ya kunshi sa ido kan waɗanda ke saya da ba a yarda da su ba da kuma yaɗa bayanai.
Haka kuma, akwai dokar rajistar bindiga - irin wadda masu motoci ke yi - a wasu daga cikin jihohin Amurka kuma hakan zai "taimaka" idan aka riƙa amfani da shi a faɗin ƙasar, a cewar Mista Kullman.
Jonathan Lowy, mai sa ido kan rikice-rikice da ke alaƙa da bindiga, ya ce ana faɗa wa masu ƙera makamai idan ana binciken bindigogi da aka yi safararsu, kuma suna snain su waye ke sayarwa musu da bindigogi.
"Idan masu ƙera bindigogi suka daina bai wa masu safararsu dama, hakan zai sa a dakatar da safarar bindigogi daga Amurka."
BBC ta tuntuɓi sashen kula da harkokin tsaron cikin gida na Amurka domin martani, sai dai ba su ce uffan ba.
Mista Le Cour ya ce an ƙara kaimi wajen sa ido kan lamarin a faɗin duniya, sai dai babu wani tasiri zuwa yanzu: "Mun san akwai matsala, kuma mun ga alamu, sai dai ba mu yin abin da ya kamata wajen magance ta".











