Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Yan wasa sun shigar da Fifa ƙara cewa ta 'mamaye komai'
Manyan Lig-Lig na Turai da ƙungiyar yan wasa Fifpro sun shigar da ƙarar hukumar kwallon ƙafa ta Duniya Fifa gaban hukumar kasashen Turai kan abin da suka kira 'mamaye komai' da hukumar ta yi
Gasanni Turai da ake bugawa guda 39 ciki har da Premeir Ingila - ƙungiyoyi 1,130 a fadin ƙasashe 33, sun yi ƙarafin Fifa na wuce gona da iri ƙarƙashin dokar nahiyar Turai ta shirya gasa, musamman idan ana maganar tsara wasannin ƙasashe ƙarƙashin Fifa.
Gasar La Liga ba ta cikin mambobin gasannin Turai amma ta shiga cikin wannan ƙorafi ita ma.
Alexander Bielefeld, shi ne daraktan tsare-tsare na Fifpro, ya ce ɓangarori daban-daban sun shigar da koke gaban gaban hukumar tarayyar Turai suna kiran abin da wanda ba su yi tsammani ba.
BBC ta yi duba kan lamarin daga duka bangarorin biyu da kuma abin da ake jayayya a kai.
Yaya aka kawo nan matakin?
Akwai turka-turkar da ke faruwa yanzu kan yawan wasannin da yan wasa ke bugawa a kaka, kuma ita ce ƙara ta baya-bayan nan da aka shigar.
Kungiyar kwararrun 'yan kwallon kafa ita ma ta bi sahun wannan ƙara kan Fifa a watan Yuni, game da yawan wasannin da ake tsara bugawa.
Kungiyar da ta 'yan wasan Faransa sun shigar da ƙarar ne a kotun kasuwanci da ke Brussels "suna ƙalubalantar halarcin hukuncin Fifa na sanya wasannin ƙasashe musamman kan hukuncin ƙirƙira da sanya kofin duniya a 2025".
An tsara za a samu wakilan Turai 12 a bikin fadada kafin duniya da za a yi a Amurka a 15 ga watan Yuni zuwa 13 ga watan Yuli.
A watan Disambar 2022 ne majalisar kolin Fifa ta tabbatar da fadada gasar inda ƙungiyar 'yan wasan ta nuna jayayyarta tana cewa "an matse komai ta yadda 'yan wasa ba za su samu damar hutawa ba yadda ya kamata tsakanin kakar da aka kammala da sabuwa".