Man City na sha'awar ɗaukar Cambiaso daga Juventus

Andrea Cambiaso.

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Manchester City na son ɗaukar ɗan ƙwallon Juventus mai tsaron baya, Andrea Cambiaso.

Wasu rahotannin na cewar ba a samu tattaunawa ba tsakanin ƙungiyoyin, yayin da a Italiya ake cewar ba tabbaci kan cinikin ɗan wasan.

Pep Guardiola na fatan ɗaukar mai tsaron baya daga gefen hagu shahararre a gurbin tun bayan Benjamin Mendy.

City ta dakatar da ɗan wasan Faransa, bayan zarginsa da laifin fyaɗe daga baya aka wanke shi da soso da sabulu a 2023.

Cambiaso, mai shekara 24, ya koma taka leda a Juventus daga Genoa a 2022, wadda ya fara yi wa wasa tun daga makarantar matasan ƙungiyar.

Ɗan wasan tawagar Italiya ya buga wasannin aro a Bologna, daga nan ya koma Juventus.

Cambiaso ya yi karawa 25 a Juventus a dukkan fafatawa a bana da cin ƙwallo biyu da bayar da biyu aka zura a raga.

City na ta kokarin yin cefane a cikin watan Janairu, bayan da tuni ake auna koshin lafiyar matashin Brazil, Vitor Reis daga Palmeiras.

Har yanzu ƙungiyar ba ta fayyace ko ta kammala cinikin ɗan ƙwallon Uzbekistan, Abdukodir Khusanov duk da cewar ta kulla yarjejniyar £33.6m da Lens kan ɗan wasan mai shekara 20.

Har yanzu City na tuntubar Eintracht Frankfurt kan sayen Omar Marmoush.

Tuni kuma Guardiola ya sanar cewar ƙyaftin, Kyle Walker zai bar ƙungiyar.