Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Zaɓen Iran: Yadda guguwar sauyi ta yi awon gaba da masu tsattsauran ra'ayi
- Marubuci, Kayvan Hosseini
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Persian
- An wallafa
A cikin ƙasa da kwana 50, Iran ta sauya daga shugaban ƙasa mai tsattsauran ra'ayi, mai adawa da ƙasashen Yamma zuwa shugaba mai sassaucin ra'ayi da kuma kawo sauyi.
Babu wanda ya yi tunanin hakan za ta faru cikin ƙanƙanin lokaci.
Shugaban ƙasar wanda aka zaɓa a ranar Asabar, Masoud Pezeshkian, ya kasance ministan lafiya a lokacin mulkin jam'iyyar masu rajin kawo sauyi ta ƙarshe a ƙasar, shekaru 19 da suka gabata.
Tun daga wancan lokaci ne aka taƙaita wa jam'iyyar masu son kawo sauyi a ƙasar damar shiga takarar shugabancin ƙasa.
Amma a wannan karo, masu son kawo sauyin sun ci gajiyar damar da suka samu.
Me ya sa hakan ya 'bayar da mamaki?'
Kundin tsarin mulkin Iran ya tanadi cewa wajibi ne Majalisar Shura ta ƙasar ta tantance duk wani mutum da ke son tsayawa takara shugabancin ƙasa.
An zargi majalisar da nuna son rai wajen irin wannan tantancewa, musamman a kan mutane masu rajin kawo sauyi, waɗanda suka yi takara a tsakanin 1997 zuwa 2005.
A manyan zaɓuka uku da suka gabata, masu rajin kawo sauyi sun koka kan cewa Majalisar Shura ta hana dukkanin manyan ƴan takararsu tsayawa takarar shugaban ƙasa, inda aka bar waɗanda ba su da ƙarfi sosai.
Saboda haka, hakan ya sanya sun kasa yin gogayya da fitattun ƴan takara na jam'iyyun masu tsattsauran ra'ayi.
A lokacin da tsohon shugaban ƙasar Ebrahim Ra'isi ya rasu sanadiyyar hatsarin jirgin sama a cikin watan Mayu, al'ummar ƙasar da dama sun yi tunanin cewa irin hakan ne zai ƙara faruwa.
Ko bayan da Majalisar Shura ta ƙasar ta sanar da sakamakon tantance ƴan takarar a zaɓen na bana, babu wanda ya yi tsammanin cewa masu neman kawo sauyin za su taka wata rawar a zo a gani a lokacin zaɓen.
Masoud Pezeshkian shi kaɗai ne ɗan takarar da ra'ayinsa ya sha bamban tsakanin ƴan takarar shugaban ƙasa shida a zaɓen: waɗanda suka kasance masu ra'ayin mazan jiya kuma suka fi karkata ga tsattsauran ra'ayi.
Jagoran addini na Iran, Ali Khamenei ya fi karkata ne ga ra'ayin ƴan mazan jiya, saboda haka dakarun juyin juya hali na ƙasar ma sun fi karkata ne kan ra'ayin ƴan mazan jiya.
A cikin shekarun nan an ga yadda masu tsattsauran ra'ayin suka tura masu ra'ayin kawo sauyi
Ƙasar ta ga yadda masu tsatsauran ra'ayi suka kori masu ra'ayin kawo sauyi daga mulki a shekarun baya-bayan nan a wani tsari na hadin gwiwa da aka fi sani da "homogenization" a kan yadda duk wanda baya goyon bayan Khamenei aka maye gurbinsa da 'yan uwansa masu ra'ayin mazan jiya.
Wannan ya haifar da gagarumin turjiya, musamman a cikin 2009 lokacin da masu neman sauyi suka ce an tafka maguɗi a zaɓen shugaban ƙasa, wanda ya sanya miliyoyin mutane suka yi zanga-zanga. IRGC da ɓangaren dakarun sa-kanta, "Basij," sun murƙushe wannan zanga-zangar da ƙarfi.
Lokacin da Ebrahim Raisi ya lashe zaɓen shugaban ƙasa a 2021, wasu manazarta sun bayyana cewa tsarin ya kammala.
Kowane ɓangare na "Jamhuriyar Musulunci" ta Iran ya faɗa ƙarƙashin ikon Shugaban addini da masu tsatsaurar ra'ayi irin ta shi, waɗanda a yanzu suke kiran kansu da ƴan kan gaba a Juyin Juya Hali.
Mista Raisi, ba kamanni iri ɗaya ne kaɗai ya ke da shi da Mista Khamenei ba, amma manufofinsa - na cikin gida da na waje - sun kasance daidai da abin da Khamenei ke ba da shawara a koyaushe: ƙoƙarin neman samun damar dogaro da kai ta fannin tattalin arziki da tsara manufofin ƙasashen waje da ake kira "a dubi Gabas,” wanda ke nufin kusantar dangantaka da China da Rasha.
Tabbas, ƙara tsaurara matsin da ke da dangantaka da “Musulunci” kan al’umma wani muhimmin ginshiki ne na manufofinsu, wanda ke nufin ƙara tsaurara matakai kan mata; manufar da ta yi sanadin mutuwar wata budurwa da ake tsare da ita a watan Satumban 2022 da kuma ɓarkewar babbar zanga-zangar adawa da gwamnatin "Jamhuriyar Musulunci" a Iran.
Martanin limaman da ke mulki ya fi zanga-zangar da aka yi a shekara ta 2009 zafi. A cewar ƙungiyoyin kare haƙƙin bil adama, a tsawon kusan watanni shida na zanga-zangar, an kashe fiye da mutane 500, ciki har da yara sama da 60 'ƴan ƙasa da shekaru 18 da ƙaruwar daƙile al'amuran intanet da kame jama'a da shari'a kan matasa masu zanga-zangar, har ma da kashe hudu daga cikinsu sun biyo bayan zanga-zangar ƙin jinin gwamnati a 2022-2023.
Sakamakon irin wannan danniya ta siyasa, zanga-zangar ta tsaya. Haka kuma, ƴan adawar gwamnati sun kasa samun daidaita kawunansu, maimakon haka sai suka cece-ku-ce a tsakaninsu wanda ya janyo rashin jituwa. Da alama gwamnatin ta yi nasarar magance babbar barazanar da ta fuskanta tun lokacin da aka kafa ta a 1979.
Sai dai zaman lafiya da aka samu bayan gagarumar zanga-zangar da ta faru a fili ne kawai. Baya ga fushin da al’umma ke yi game da murkushe masu zanga-zanga, matsin tattalin arziki daya ne daga cikin abubuwan da suka taka muhimmiyar rawa.
Saboda haka nan lokacin da labarin rasuwar Shugaba Ebrahim Ra’isi ya bullo, gudanar da wani zaben shugaban kasa ya zamo wani fashin hankali ga jagororin kasar.
Amma mutanen da suka gaza bayyana adawa da fushinsu da kuma yan adawa - wadanda yanzu suke da jajirtattun mutane kamar wadda ta lashe kyautar Nobel, Narges Mohammadi, wadda yanzu ke a gidan yari - zaben ya zame masu wata hanyar nuna fushi da kaurace wa zabe cikin lumana.
Duk da haka, masu neman kawo sauyi - musamman manya daga cikin su kamar tsohon shugaban kasar Mohammad Khatami - suka yi kokarin sauya salon su na rashin daukan zaben da muhimmanci, inda a wannan karo suka bayar da gagarumar gudumawa wajen mara wa Masoud Pezeshkian baya. Wannan ya sanya da farko ya zamo tamkar gwagwarmaya ce tsakanin masu karfafa wa mutane gwiwa su yi zabe da kuma wadanda ke neman a kaurace.
Wannan ya sanya aka samu mafi kankantar mutanen da suma fita kada kuri’a a tarihin zaben kasar: kimanin kashi 40 cikin dari ne kawai suka fita kada kuri’a a zagayen farko, inda yan takara biyu da suka yi zarra suka je zagaye na biyu: wato Masoud Pezeshkian da Saeed Jalili, wanda mai tsattsauran ra’ayi ne, wanda a baya ya rike mukamin babban mai wakiltar Iran a tattaunawa kan makamashin nukiliya daga lokacin mulkin Mahmoud Ahmedinajad har zuwa shekara ta 2013.
Duk da kasancewar Mista Jalili a matsayin wanda ra’ayinsa ya yi daidai da na jagiran addini na kasar, da kuma rade-radi kan rashin ingancin zaben, a ranar Asabar duniya ta wayi gari da cewa Mista Pezeshkian shi ne sabon zababben shugaban Iran; mutumin da ya yi alkawarin kawo sauyi a kusan dukkanin bangarorin da suka shafi rayuwar al’ummar kasar.
Waɗanne alƙawurra Pezeshkian ya ɗauka?
Mista Pezeshkian ya gina yakin neman zabensa ne kan sukar tsarin masu tsattsauran ra’ayi na adawa da kasashen Yamma. Tare kuma da hada tawagar gogaggun ‘yan siyasa masu rajin kawo sauyi, inda ya dauko Mohammad Javad Zarif, ministan harkokin waje na kasar wanda ya jagoranci tattaunawa kan yarjejeniyar nukiliya a 2015.
Duk da cewa Mista Zarif ba ya cikin na gaba-gaba a harkar kawo sauyi, amma ya taka muhimmiyar rawa wajen fafutikar ganin an zabi Pezeshkian.
A cikin kudurorin da ya dauka, Mista Perzeshkian - yayin da suke tsaye tare da Zarif a gefensa ya bayyana cewa manufofinsa kan harkokin waje ba za su kasance na “kiyayya da Yamma” ko “kiyayya da Gabas ba.”
Dukkanin mutanen biyu sun soki lamarin marigayi Ebrahim Ra’isi wanda suka ce yana kokarin kulla alaka da Rasha da kuma China, sannan sun bayyana cewa su ne kadai za su iya shawo kan matsalar tattalin arzikin kasar ta hanyar tattaunawa da kasashen yamma domin samar da mafita ga rikita-rikitar shirin nukiliyar kasar da kuma kokarin ganin an sassauta takunkuman da ke kanta.
Abin da dayan dan takaran da kuma jagoran addini na kasar suka yi alla-wadai da shi.
Khamenei ya bayyana masu tunanin cewa gyara alaka tsakanin kasar da kasashen yamma zai kawo wa kasar ci gaba a matsayin “wadanda suka bata,” yana magana kan yarjejeniyar nukiliyar da Amurka ta janye daga ciki duk da kiyayewar da Iran ta yi.
Ra’ayinsa kan manufofin kasashen waje na kasar na da tasiri sosai saboda irin karfin da kundin tsarin mulki ya ba shi da kuma ra’ayinsa kan harkokin waje.
Mista Pezeshkian da tawagarsa sun fuskanci kalubale sosai sanadiyyar masu kira da a kaurace wa zaben, wadanda ke ganin cewa shugaban kasa ba ya da karfin ikon sauya manufofin kasashen waje na kasar a irin tsarin tafiyar da mulki na Iran; wani ikirari mai tushe.
Daya daga cikin bangarori mafiya muhimmance wajen samar da tsarr-tsare a yankin su ne Dakarun Qudus. Amma shugaban kasa bai da iko kai tsaye a kansu kuma jagoran addini ne kawai ke da ikon ba su umurnin su yi ko kada su yi.
Sai dai duk da haka, shugaban kasa shi ne babban jami’in gwamnati a bangaren diflomasiyya, kuma ba ofishinsa kadai ba, ma’aikatar harkokin waje ma na taka muhimmiyar rawa wajen aikwatar da manufofin. Suma da damar bi ta bayan gida wajen ganin an biya musu bukatunsu - kamar yadda ya faru a 2015 lokacin da shugaban kasar Hassan Rauhani mai matsakaicin ra’ayi ya shawo kan gwamnati, ciki har da Mista Khamnei wajen ganin an amince da yarjejeniyar nukiliya.
Haka nan kuma gwamnati za ta iya yin tasiri wajen neman goyon bayan manufofi wadanda ba lallai ne su yi daida ba dari bisa dari da manufofin jagoran Islama na kasar ba.
Wadannan ne kawai hanyoyin da masu neman kawo sauyi za su iya bi su cika alkawuran da suka dauka tare da kawo karshen abin da Pereshkian ya bayyana a matsayi “katangar da masu tsattsauran ra’yi suka gitta.”
Sai dai a wannan karo, ba kamar sauran gwamnatocin masu rajin kawo sauyi da aka yi a baya ba - za a iya cewa babu alkawurran da suka yi game da samar da ‘yanci da walwalar al’umma ba.
Masu fafutikar kawo sauyi sun fuskanci mummunan danniya ta siyasa, ciki har da kisan manyan fasihansu, da rufe gidajen jaridu da gurafanar da tarin yan siyasa a kotu.
Ba su da karfi a muhimman bangarorin tafiyar da mulki, kamar a ofishin jagoran addini na kasar, da kwamitin shura da kuma majalisar koli ta tsaro ta kasar.
Ba za su iya gudanar da zabuka ba, ko canza dokokin tacewa ba ko kuma bai wa dakarun Hisba na kasar umarni ba.
Sannan ba kamar zaben shekara 27 da suka gabata ba, inda sama da mutum mikiyan 20 suka zabe su ba (daga cikin masu kada kuri’a 35), Pershkian a nasa bangaren ya lashe zabe ne da kuri’a miliyan 16, daga cikin mutane mikiyan 62 wadanda suka cancanci kada kuri’a.
Sama da mutum milayan 13 duk sun zabi dan takarar shugaban kasar ne mai tsattsauran ra’ayi, Saeed Jalili, wanda ya bayyana cewa ya kamata irin ta kara zafafa adawarta da Kasashen Yamma domin kare muradunta.