Kayatattun hotunan Afirka na wannan mako

An wallafa

Mun zabo muku kayatattaun hotunan Afirka da 'yan Afirka a wasu nahiyoyin na wannan makon:

Wasu 'yan mata

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wadannan 'yan matan na cikin mutanen da ke yin hijira daga Madera a kasar Kenya ranar Juma'a, bayan fari ya addabi yankin. Yanzu haka yankina yana fama da fari mafi girma cikin shekaru arba'in, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane da dabbobi...
Rakuma

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Dabbobi, cikinsu har da wadannan rakuman, na yin hijira. An kwashe damuna hudu ba a yi ruwan sama ba a wasu yankunan Kenya, lamarin da ya haifar da fari.
Yara

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A can Nairobi da ke Kenya, wadannan yaran suna yin gwajin rawa salon ballet. Ranar Asabar an gayyaci yara 500 zuwa National Theatre domin kallon The Nutcracker...
Wasu 'yan mata da ke rawa

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Wadannan 'yan matan sun yi rawa a gasar Rawa ta Dance Centre Kenya (DCK) tare da tawagar Nairobi Philharmonic Orchestra.
Ballerina tana shafa jan-baki

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, An gudanar da gasar rawa a wasu yankuna na nahiyar inda a Dakar, mai rawa 'yar kasar Rasha ta shafa jan-baki a mazauninta kafin ta shiga gasar The Nutcracker ranar Litinin. 'Yan kasar Rasha masu rawa bakwai ne suka je Dakar domin taka rawa tare da Slou Akimguereeva.
Masu tallan kayan kawa

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Kazalika an yi gasar kayan kawa a Senegal, mai taken Dakar Fashion Week ranar Asabar. Wannan ne karo na 20 da aka gudanar da wannan gasa...
Masu ado don yin gasa

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A gefe guda, wasu masu gasar kayan kawa sun tsaya suna jira.Wadanda suka shiga gasar sun fito daga Afirka ta Kudu, Mali, Mozambique da sauran kasashe, a cewar shafin intanet na Africa News.
Wasu 'yan mata

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An ci gaba da bikin nuna kayan kawar a Afirka ta Kudu a makon Kayan Kawa na Soweto Fashion Week ranar Juma'a
Nigerian women wearing the same green and yellow printed dresses walking the streets.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Wasu 'yan siyasa da ke goyon bayan dan takarar shugaban Najeriya a zaben 2023, Atiku Abubakar na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) sun yi gangami a Legas
Boy with a large Moroccan flag standing in the street.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wani yaro ya daga tutar Morocco a Sifaniya, gabanin fafatawar da kasarsa za ta yi a gasar cin Kofin Duniya...
A woman with long hair posing with a Moroccan flag. She is smiling and there is a jubilant crowd of men in the background.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, An yi shagulgula a Morocco da biranen kasashen Turai da dama irin su Brescia da ke Italiya bayan Morocco ta yi nasara da 3-0 a bugun fenareti...
Masu murna

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Kazalika an gudanar da shagulgula a Paris.
Naomi Campbell ta gana da shugaban  Senegal - Macky Sall.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Fitacciyar mai tallata kayan ƙawa 'yar Birtaniya Naomi Campbell ta gana da shugaban Senegal Macky Sall a Dakar. Babu tabbaci ko sun tattauna a kan gasar Kofin Duniya tsakanin Senegal da Ingila, amma Ms Campbell ta halarci bikin nuna kayan kawa na Dakar Fashion Week, a cewar mujallar British Vogue...
Fan wearing colours of the Senegal flag in a crowd of people watching the football.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wata 'yar kasar Senegal da ta je Qatar don kallo fafatawar da kasarta ta yi, ko da yake abin takaici Ingila ta doke Senegal da ci 3-0
Sope Williams

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Farfesa a fanni shari'a da ke fafutukar yaki da cin hanci 'yar Najeriya Sope Williams ta dauki hoto a yayin da ta lashe kyautar Sheikh Tamim Bin Hamad Al-Thani International Excellence Award a Qatar. Ana bayar da kyautar ne ga mutanen da ke yaki da cin hanci

Dukkan hotunan suna da hakkin mallaka.