Arteta ya ci Man City a karon farko a wasa na takwas a Premier

Asalin hoton, Getty Images
Arsenal ta yi nasara a kan Manchester City da ci 1-0 a wasan mako na takwas a gasar Premier League da suka kara a Emirates ranar Lahadi.
Tun farko sun je hutu ba ci kuma karon farko da hakan ta faru tsakanin ƙungiyoyin tun bayan Afrilun 2012, kuma a lokacin Gunners ce ta ci wasan ta hannun Mikel Arteta a lokacin yana buga mata tamaula.
Daf da za su tashi wasan ne Arsenal ta ci kwallo ta hannun Gabriel Martinelli, saura minti huɗu lokaci ya cika.
Arsenal ta yi fafatawar ba tare da Bukayo Saka ba, karon farko da bai buga mata Premier League ba, wanda ya yi karawa 87 a jere a babbar gasar tamaula ta Ingila.
Shi ne kan gaba a irin wannan yawan buga Premier League a jere a tarihin wasannin.
Da wannan sakamakon Arrsenal tana mataki na biyu a kan teburin Premier League da maki 20, iri ɗaya da na Tottenham, wadda take ta ɗaya.
Ranar Asabar Tottenham ta ci Luton 1-0 a wasan mako na takwas a babbar gasar tamaula ta Ingila.
Kawo yanzu ba a doke Tottenham da Arsenal ba daga wasa takwas da aka fara a Premier League.

Asalin hoton, BBC Sport











