Zan saka ƙwazon aiki a matsayin hanyar samun ci gaba a aikin soji - Ɗan takarar SDP Adebayo

Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon cikakkiyar hirar
Zan saka ƙwazon aiki a matsayin hanyar samun ci gaba a aikin soji - Ɗan takarar SDP Adebayo
An wallafa

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar SDP Adewole Adebayo ya ce Abin da Najeriya ke nema shi ne kyakkyawan hali da ƙwazo da burin cimma muradi.

Mista Adebayo lauya ne kuma shekararsa 50 da haiuwa kuma ɗan asalin Jihar Ondo ne da ke kudancin Najeriya.

Ya bayyana cewa takararsa ta farko ita ce ta shugaban ƙasa kuma ya fito takarar ne domin ya warware matsalolin da ƙasar ke ciki.