Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Toni Kroos ya buga wa Real Madrid wasa na 400
Real Madrid ta doke Espanyol 3-1 a wasan mako na 25 a gasar La Liga ranar Asabar a Santiago Bernabeu.
Tsohon dan kwallo tawagar Jamus, Toni Kroos ya buga wa Real wasan, kuma na 400 da ya yi wa kungiyar kenan.
Real Madrid tana mataki na biyu da tazarar maki shida tsakaninta da Barcelona ta daya a teburi, wadda ta ziyarci Athletic ranar Lahadi a gasar La Liga.
Tun bayan da dan kasar Jamus ya koma Sifaniya da murza leda a 2014, ya zama kashin bayan Real Madrid a jerin masu buga mata wasa daga tsakiya.
Kawo yanzu ya dauki Champions League hudu da Club World Cup biyar da European Super Cup hudu da La Liga uku da kuma Spanish Super Cups uku.
Kroos shine dan kasar Jamus da ya kafa tarihin yawan buga wasanni a Real Madrid kawo yanzu.
Ga jerin wasa 400 da ya yi a Real Madrid:
- Wasa 263 a La Liga
- Wasa 93 a Champions League
- Wasa 20 a Copa del Rey
- Wasa 11 a Spanish Super Cup,
- Wasa 9 a Club World Cup
- Wasa 4 a European Super Cup
Toni Kroos ya zura kwallo 27 a raga, an kuma yi nasara da shi a karawa 255 a Real Madrid.