Hanyoyi biyar da za ku rage wa kanku raɗaɗin matsin rayuwa
Hanyoyi biyar da za ku rage wa kanku raɗaɗin matsin rayuwa
An wallafa
Ganin yadda al'amura ke ƙara ƙamari a Najeriya, masana harkokin tattalin arziki da na zamantakewa na bai wa mutane shawarar yadda za su rage wa kansu raɗaɗin halin da ake ciki.
Murtala Adogi Muhammad, masani kan tattalin arziƙi ya bayar da shawarawari biyar da 'yan Najeriya za su bi a irin wannan hali.
A ranar Litinin ne Hukumar Ƙididdiga ta Najeriya ta ce hauhawar farashi ta kai kashi 33 cikin 100 a watan Maris, yayin da hauhawar farashin kayan abinci ta kai kashi 40 cikin 100.
A gefe guda kuma, gwamnatin Shugaba Bola Tinubu na ci gaba da ɗaukar matakan tattalin arziki da suka haɗa da cire tallafi a ɓangarori da dama, amma ta ce tana aiki tuƙuru wajen sauko da farashin kayayyakin.



