Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Man United za ta sayar da Antony Arsenal za ta sayo mai cin kwallaye
Manchester United na shirin sayar da dan kwallon Brazil, mai shekara 24, Antony, yayin da take son maye gurbinsa da Michael Olise na Crystal Palace. (Rudy Galetti via X)
Manchester United za ta tanadi £80m, domin zawarcin dan kwallon Everton mai tsaron bayan tawagar Ingila ta matasa 'yan kasa da shekara 21, Jarrad Branthwaite. (Sun)
Inter Milan na son taya dan kwallon Manchester United mai tsaron bayan tawagar Ingila, Aaron Wan-Bissaka, mai shekara 26, idan mai shekara 27 dan kasar Netherlands, Denzel Dumfries ya bar kungiyar a bana. (Gazzetta dello Sport - in Italian)
Za a bai wa kociyan Sporting Lisbon, Ruben Amorim lokacin mai tsawo kan salo da tsarin da zai dora Liverpool idan ya maye gurbin Jurgen Klopp a kaka mai zuwa. (Football Insider)
Arsenal na son sayen mai cin kwallaye a badi domin yin gogayya da dan kwallon Brazil, Gabriel Jesus, mai shekara 27 da dan kasar Jamus, Kai Havertz, mai shekara 24, cikin wadanda take son tuntuba har da dan wasan Bologna, Joshua Zirkzee, mai shekara 22. (TeamTalk)
Watakila Manchester United ta yi kokarin sayen dan wasan Brentford, mai shekara 28 dan kwallon tawagar Ingila, Ivan Toney a kaka badi. (Mirror)
Tottenham da West Ham da kuma AC Milan na rige-rigen daukar dan wasa Fulham mai shekara 26 mai tsaron bayan tawagar Ingila, Tosin Adarabioyo idan kwantiraginsa ya kare a karshen kakar bana. (Mirror)
Tsakanin Fulham ko West Ham na son taya dan kwallon Panathinaikos mai shekara 24 dan kwallon Girka, Fotis Ioannidis, wanda aka ce ya kai darajar kudi £15m. (Sun)
Tottenham na shirin kara sa kaimi domin sayen dan wasan Atalanta dan kasar Brazil mai shekara 22, Ederson. (TeamTalk)