Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Akwai wani abu da zai sauya a Rasha bayan rantsar da Putin a karo na biyar?
- Marubuci, By Steve Rosenberg
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Russia editor
- An wallafa
Ko da ido rufe zai iya tafiyar da mulkin Rasha.
A karo na biyar, Vladimir Putin ya sha rantsuwar kama mulki a ƙasaitacciyar fadar shugaban ƙasa ta Kremlin, inda zai ci gaba da jagorantar ƙasar na tsawon shekara shidda.
Duk da cewa kusan an san duk wani abu da zai iya wakana, amma abubuwa da dama sun sauya tun daga watan Mayu na shekarar 2000, sa'ilin da Putin ya sha rantsuwa a karon farko.
A wancan lokaci shugaba Putin ya yi alƙawarin "karewa da bunƙasa mulkin demokuraɗiyya" da kuma "kulawa da Rasha".
Shekara 20 bayan haka, Putin ya ƙaddamar da yaƙi a kan Ukraine; lamarin da ya haifar wa Rasha asara mai yawa.
A cikin gida kuma, a maimakon ya mayar da hankali wajen bunƙasa demokuraɗiyya, Putin ya ci gaba da raunana ta ne: yana ɗaure masu adawa da shi, da kawar da duk wata dokar da za ta bayar da damar sanya masa ido.
"A yanzu Putin na kallon kansa a matsayin wani gwarzo a tarihin Rasha," in ji Fiona Hill, tsohuwar mai bai wa shugaban Amurka shawara kan tsaro.
"Idan muka koma duba baya, wa'adi biyu na farkon shugabancin Putin, za mu iya cewa babu laifi game da mulkin Putin. Ya daidaita tattalin arziƙin ƙasar tare da sake mayar da ita mai dogaro da kai. Tattalin arziƙin Rasha ya riƙa bunƙasa fiye da kowane lokaci a tarihi.
"Amma yaƙin Ukraine da kuma ƙwace yankin Kiremiya shekara 10 da suka wuce sun karkatar da ƙasar daga turba. Ya mayar da kansa ɗan danniya a madadin mai adalci."
Tun bayan kama mulkin Vladimir Putin a Rasha, Amurka ta yi shugaban ƙasa guda biyar yayin da Birtaniya ta yi firaiminista bakwai.
Bayan shafe kimanin ɗaya cikin huɗu na shekarun ƙarni guda, tabbas Putin ya shiga tarihi.
A baya, da wahala ka ji mutane na magana kan aƙidar "Brezhnevism", wato duk wata barazana ga ɗaya daga cikin ƙasashen Soviet...barazana ce ga dukkanin ƙasashen, ko aƙidar "Gorbachevisim" ko kuma ta "Yeltsinism".
Akwai wani sabon tsarin jagoranci da yanzu ake kira Putinism.
Andrei Kolensnikov, jami’i a cibiyar nazari kan yankin Rasha da Asiya ya ce “Yanzu mun ƙara samun wani salon jagoranci wanda yake kamancece niya da tsarin Stalism na tsohon jagoran Tarayyar Soviet, Stalin”.
“Zan iya cewa salon mulkin Putin ya yi daidai da na Stalin. Yana abubuwansa kamar yadda Stalin ke yi. Kuma kamar Stalin, yana so ya ci gaba da kasancewa a kan mulki har ƙarshen rayuwarsa.”