'Yar da ta sha alwashin gano mahaifinta bayan ta zargi gwamnatin Iran da sace shi

An wallafa

Bayan shekara biyu yana buya, a watan Disambar 2021 Ebrahim Babaei ya yanke shawarar tserewa daga Iran.

Mai shekara 57 wanda aka ɗaure saboda siyasa, ya shahara wajen adawa da sugabanci irin na addinin Islama, ya samu wasu masu safarar mutane suka yi masa alƙawarin za su fitar da shi daga ƙasar zuwa iyakar arewa maso yammaci kan iyakar Turkiyya.

Akai-akai Ebrahim na magana da 'yarsa ta waya, wadda mai fafutikar kare haƙƙin ɗan Adam ce da ke gudun hijira a Belgium, har zuwa lokacin da ‘yan fasa ƙaurin suka ɗauke shi zuwa wani ƙauye da ke kan iyakar.

“Mahaifina a tsorace yake shi yasa yake magana a hankali. Sun kai kusan su 25 da aka zuwa a cikin rumbu. Ya yi alƙawarin kirana da zarar sun tsallaka kan iyaka,” in ji Shima.

Amma tun daga nan ba ta ƙara ji daga mahaifinta ba.

Haka ma abokanta da take cewa su gaida mahifin nata ba wanda yaji daga gare su.

Masu safarar mutanen sun ce mata mahaifin nata ya mutu ne a gidan wani mai sumoga a kusa da ƙauyen Van kuma gawarsa na hannun ‘yan sandan Turkiyya.

Bayan ‘yan kwanaki, wani mai safarar mutane ya kira waya ya yi iirarin cewa ya mutu sakamakon bugawar zuciya a ƙauyen Ozalp da ke kan iyakar Turkiyya, anan kuma aka binne shi.

“Na girgiza na yi shiru na gaza cewa komai,” in ji Shima “kawai sai na ji na fasa ihu ina cewa Baba kana ina ne?”

‘Yan sanda Turkiyya da masu tsaron iyaka da jami’an asibiti da wurin ajiye gawa sun ce ba su samu wata gawa da za ta yi daidai da bayanan da aka bayar na Ebrahim ba, kuma a binciken da suka yi ba su tsallako iyaka ba, kamar yadda suka shaida wa lauyoyin gidansu Shima.

Iyalansa sun kai rahoton ɓatansa wajen hukumomin Iran.

Amma ‘yan sanda da lauyoyi sun ce an yi buris da maganar ba tare d gudanar da wani bincike ba.

Kusan shekara guda da ta gabata, BBC Fasha ta fara gudanar da bincike kan ɓatan Ebrahim amma ba su samu hujjar komai ba game da tsallakawarsa Turkiyya, ya mutu kuma an binne shi a Ozalp.

Bayan kallon tattaunawar da muka yi da Shima a watan Unin bara, wani ɗan iran mai neman mafaka a in Switzerland ya neme mu ya ce suna tare da Ebrahim ranar daga ita ba a sake ganinsa ba.

Matashin da yake cikin shekarunsa na 20, ya ce suna tare da wasu Iraniyawa da ‘yan Afghanistan 25 domin tsallaka iyakar Turkiyya ranar 21 ga Disambar 2021.

Ya ce dakarun Iran ne suka kama su kafin su isakan iyakar.

Wani mai safara ya shaida wa BBC cewa mafi yawan waɗan ya kwaso ashe suna da alaƙa da jami’an tsaron Iran.

Ya ce su ka mika ‘yan adawa zuwa ga hukumomi, su kuma a na su bangaren jami’an leken asirin sai su sai su kyalle su cigaba da safarar miyagun kwayoyi da mutane daga Afghanistan zuwa Turkiyya.

Ebrahim tsohon sojan kasar Iran ne wanda a ka yi gwagwarmaya da shi a yakin da aka y da iran. Amma sai a ka yi masa mummnan hukunci a lokacin da ya juya wa gawamnatin baya, kaman yadda jamhoriyar ta saba yi wa tsoffin magoya bayan ta.

Amnesty International ta ce Ebrahim ,ya fuskanci abubuwa da dama sakamakon gwagwarmayar siyasar da ya yi, wanda su ka hada da kama shi ba tare dalili ba, tsare shi ba bisa ka’ida ba, a ka gufanar da shi a kotu, da kuma azabtarwa.

Tun da mahaifin ta ya bace, Shima ta fara yakin neman hukumonmin kasan Iran su yi bayanin abun da ya faru da shi.

Cikin ‘yan watannin da su ka wuce, da ita da wadansu mata masu fafutukar neman ‘yanci, sun hadu da shugaban kasar faransa, Emmanuel Macron a birnin Paris.

"Na fada wa shugaba Macron cewa a duk minti daya da yammacin duniya ta kyale Jamhuriyar Iran akwai iyali irin ta wa da ke shan wahala. Alhakkin abin da ke faruewa a Iran na hannun ku. Yammacin duniya ya kamata su dauki shugabannin Iran tamkar kaman yadda su ka dauki shugaban kadsar Rasha Vladimir Putin.

Ebrahim na daya daga cikin daruruwan ‘yan adawan gwamnatin Iran da kuma masu fafutukar kare hakkin bil adama da a ka kwashe shekaru a na daure su, da sace su taer da batar da su baki daya.

Ana tsoron cewa an kashe su bayan an azabtar da su, kuma binne a asirce. Amma mafi yawanci iyalen su na sa ran cewa za su iya dawowa gida.

"Ban san inda mahaifi na ya ke ba, ko abun da ya ke ci, ko kayan da ya ke saka wa. Ina bakin cikin kadaicewan sa. Na gaji da wannan lamarin, amma har yanzu ina sa ran cewa zan sami labari mai dadi a kan sa.” Shima ta ce