Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Yan Barca da za su kara da Inter a Champions League
Ranar Laraba Barcelona za ta karbi bakuncin Inter Milan a wasa na hudu a cikin rukuni na uku a Champions League da za su kara a Camp Nou.
Ranar Talata 4 ga watan Oktoba, Inter ta yi nasara a kan Barcelona da ci 1-0 a fafatawar da suka yi a San Siro.
Wannan shi ne wasa na 16 da za su kara a gasar zakarun Turai, bayan da Barcelona ta yi nasara a takwas da canjaras hudu, Inter ta ci uku daga ciki.
Bayern Munich ce ta daya a rukuniin mai maki tara, sai Inter Milan da maki shida, Barcelona maki uku ne da ita da kuma Viktoria Plzen, wadda ba ta da maki.
Tuni kociyan Barcelona, Xavi ya bayyana 'yan wasa 21 da zai fuskanci kungiyar Italiya.
'Yan kwallon sun hada da Ter Stegen, Piqué, Sergio, O. Dembélé, Pedri, Lewandowski, Ansu Fati, Ferran, Marcos A., Jordi Alba, Kessie, S. Roberto, F. De Jong.
Sauran sun hada da Raphinha, Eric, Iñaki Peña, Balde, M. Casadó, Gavi, Pablo Torre and Arnau Tenas. Out through injury are Bellerín, R. Araujo, Memphis, Christensen da kuma Kounde.