Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An ci Bayern Munich a karon farko a Bundesliga ta bana
Bayern Munich ta yi rashin nasara a karon farko a bana a gidan Augsburg ta barar da damar hawa kan teburin Bundesliga.
Mergim Berisha ne ya ci kwallon, wanda ya bai wa kungiyar nasarar farko a gida a kakar nan.
Kawo yanzu Bayern ta kasa cin wasa hudu a babbar gasar tamaula ta Jamus, watakila ta fice daga jerin hudun farko idan an kammala wasanni Lahadi.
Borussia Dortmund ta hau kan teburin Bundesliga, bayan da ta yi nasara a kan Schalke da ci 1-0.
Youssoufa Moukoko, mai shekara 17, shi ne ya ci kwallon da ya bai wa kungiyar da Edin Terzic ke jan ragama nasara,, ya zama matashin da ya ci kwallo a gasar.
Union Berlin, wadda take ta biyu za ta iya komawa matakinta na daya idan ta doke Wolfsburg ranar Lahadi, wadda take ta uku Freiburg za ta ziyarci Hoffenheim a ranar.
Wasannin da Bayern Munich tta buga a bana:
German Super Cup Asabar 30 ga watan Yuli
- RB Leipzig 3 - 5 B Munich
Bundesliga Juma'a 5 ga watan Agusta
- E Frankfurt 1 - 6 B Munich
Bundesliga Lahadi 14 ga watan Agusta
- B Munich 2 - 0 Wolfsburg
Bundesliga Lahadi 21 ga watan Agusta
- Bochum 0 - 7 B Munich
Bundesliga Asabar 27 ga watan Agusta
- B Munich 1 - 1 B M'gladbach
German Cup We 31Aug 2022
- Viktoria Koln 0 - 5 B Munich
Bundesliga Asabar 3 ga watan Satumba
- Union Berlin 1 - 1 B Munich
Champiions League Laraba 7 ga watan Satumba
- Inter 0 - 2 B Munich
Bundesliga Asabar 10 ga watan Satumba
- B Munich 2 - 2 Stuttgart
Champiions League Talata 13 ga watan Satumba
- B Munich 2 - 0 Barcelona
Bundesliga Asabar 17 ga watan Satumba
- Augsburg 1 - 0 B Munich