Abin da ya kamata ku sani kan wasan United da Palace a League Cup

League Cup

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Manchester United za ta karbi bakuncin Crystal Palace a wasan zagaye na uku a Carabao Cup ranar Talata.

United na fatan 'yan wasanta da ke jinya, za su koma buga mata wasanni, yayin da Raphael Varane da Sofyan Amrabat suka buga mata wasa ranar Asabar.

Kungiyar da Erik ten Hag ke jan ragama ta yi nasara a kan Burnley da ci 1-0 a Turf Moor a wasan mako na shida na Premier League.

Lisandro Martinez bai samu zuwa gidan Burnley ba, Jonny Evans ya maye gurbinsa, Sergio Reguilon kuma ba shi da lafiya, in ji kocin United.

United za ta buga karawar da kwarin gwiwa a Old Trafford, bayan ta ci Burnley 1-0 ranar Asabar, ita kuwa Palace da Fulham sun tashi 0-0.

Labari mai dadi daga United, inda ''yan wasa biyu da ke jinya suka fara zuwa atisaye ciki har da Mason Mount.

Tsohon dan kwallon Chelsea ya yi jinya mako biyar, kuma rabon da ya buga tamaula tun cikin watan Agusta a karawar Firimiya da Tottenham ta doke United.

Haka shi ma, Harry Maguire yana cikin 'yan wasan United da suka yi atisaye ranar Lahadi, amma bai buga karawarsu da ta yi da Bayern Munich ba, da kuma ta Burnley.

Kawo yanzu wadanda suka dade suna jinya a United sun hada da Tyrell Malacia da Luke Shaw da Aaron Wan-Bissaka, har da matashi Amad da kuma Kobbie Mainoo da aka bai wa damar buga tamaula.

Wasu matasan da ake ganin watakila su buga Carabao Cup a United ranar Talata sun hada da Alejandro Garnacho da kuma Facundo Pellistri.

Watakila mai tsaron raga, Altay Bayindir ya fara yi wa kungiyar tamaula, idan Ten Hag ya so sauya mai tsaron raga.

Labari da ya shafi Crystal Palace:

Wasan da suka buga bara a Premier League 2022/2023

Asabar 4 ga watan Fabrairun 2023

Man Utd 2 - 1 Crystal Palace

Laraba 18 ga watan Janairun 2023

Crystal Palace 1 - 1 Man Utd

Manchester United ce ke rike da Carabao Cup na bara,

Roy Hodgson

Asalin hoton, Getty Images

Watakila Palace ta buga wasan ba tare da Michael Olise ba, wanda ya ci Liverpool kwallo mai ban sha'awa a bugun tazara cikin watan Janairu.

Ana cewa mai shekara 21 zai koma fagen fama ne a watan Oktoba bayan wasannin duniya.

Sauran 'yan wasan da ke jinya sun hada da sabon dan kwallon da ta dauka bana Jefferson Lerma da Matheus Franca, amma dai da kyar ne, idan Naouirou Ahamada zai yi fafatawar.

Haka kuma koci, Roy Hodgson na jiran likitocin Palace idan sun kammala auna koshin lafiyar Odsonne Edouard.

James Tomkins ma na jinya, sai dai Marc Guehi ya buga gasar Premier ranar Asabar, inda suka tashi ba ci da Fulham.

Wasannin zagaye na uuku da za a buga a Carabao Cup ranar Talata 26 ga watan Sattumba

  • Bradford City da Middlesbrough
  • Ipswich Town da Wolverhampton Wanderers
  • Port Vale da Sutton United
  • Mansfield Town da Peterborough United
  • Exeter City da Luton Town
  • Salford City da Burnley
  • Manchester United da Crystal Palace