Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Odegaard ne gwarzon Afirilu da magoya bayan Arsenal suka zaba
Martin Odegaard shine ya lashe kyautar gwarzon kwallon kafa da magoya bayan Arsenal suka zaba na watan Afirilu.
Karon farko kenan da dan kwallon ya lashe kyautar wata-wata a bana da magoya baya kungiyar kan zabo mafi kokari a wasannin Gunners.
Kyaftin din ya samu kuri'a kaso 68 cikin 100, sai Gabriel Martinelli na biyu da kuma Ben White na uku.
Martin wanda ya taka rawar gani a watan Afirilu ya ci West Ham United kwallo mai kayatarwa da wadda ya zura a ragar Southampton.
Haka kuma shine ya bai wa Granit Xhaka kwallon da ya ci Leeds United, wanda ya raba tamaula kaso 86 cikin 100 a karawa biyar da ya yi wa Gunnewrs a cikin Afirilu.
Gwarzon wata-wata a Arsenal a kakar 2022/23
Agusta: Gabriel Jesus
Satumba: Granit Xhaka
Oktoba: Granit Xhaka
Nuwamba: Ben White
Disamba: Bukayo Saka
Janairu: Oleksandr Zinchenko
Fabrairu: Oleksandr Zinchenko
Maris: Leandro Trossard
Afirilu: Martin Odegaard