Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Real Madrid ta yi waje da Chelsea a Champions na bana
Real Madrid ta kai karawar daf da karshe a Champions League na bana, bayan da ta doke Chelsea 2-0 ranar Talata a Stamford Bridge.
Rodrygo ne ya ci wa Real kwallayen ta farko minti 13 da komawa zagaye na biyu ya kuma kara na biyu saura minti 10 a tashi daga wasan.
Kungiyar Sifaniya ta kai zagayen gaba da cin kwallo 4-0 gida da waje, bayan da ta zura 2-0 a ragae Chelsea ranar 12 ga watan Afirilu a Santiago Bernabeu.
Karo na 11 da Real Madrid ta kai daf da karshe daga Champions League 13 da ta buga a baya.
Chelsea ta kasa cin kwallo a wasa biyu a jere a Champions League a karon farko tun bayan haduwa da Chelsea a 2004/05, kuma Lampard ya buga wasa biyun.
Real ce mai rike da kofin bara, kuma na 14 da take da shi jimilla, kuma ita ce ta yi waje da Liverpool a zagaye na biyu da cin 6-2 gida da waje.
Karo hudu a jere Lampard na shan kashi kenan tun bayan da ya karbi kungiyar a matakin rikon kwarya, bayan shekara biyu da ta kore shi.
Lampard ya yi rashin nasara a hannun Wolverhampton a wasan farko da ya ja ragama a rikon kwarya a gasar Premier League, bayan da ya maye gurbin Graham Potter.
Ya kuma sha kashi a gidan Real Madrid, sannan Brighton ta ci Chelsea 2-1 a Premier League ranar Asabar wasan mako na 31.
Karon farko Chelsea ta yi rashin nasara a wasa hudu a dukkan karawa tun bayan Nuwambar 1993.
Wasa tsakanin Real Madrid da Chelsea
2022/23 Champions League
- Chelsea 2 - 0 Real Madrid
- Real Madrid 2 - 0 Chelsea
2021/2022 Champions League
- Real Madrid 2 - 3 Chelsea
- Chelsea 1 - 3 Real Madrid
2020/2021 Champions League
- Chelsea 2 - 0 Real Madrid
- Real Madrid 1 - 1 Chelsea
1998/1999 European Super Cup
- Chelsea 1 - 0 Real Madrid
1970/1971 Euro Cup Winners Cup
- Chelsea 2 - 1 Real Madrid
- Chelsea 1 - 1 Real Madrid
Chelsea wadda take mataki na 11 a teburin Premier da kyar idan za ta buga gasar Zakarun Turai ta badi ta Champions ko Europa ko kuma Conference League a irin wannan matakin.
Kungiya ta daya zuwa ta hudu ke wakiltar Ingila a Champions League, yayin da ta biyar da ta shida ta buga Europa League ta bakwai ta fafata a Conference League..
Kungiyar wadda ke kan gaba a wajen kashe kudi wajen cefanen 'yan wasa a bana ta kasa daukar kofi koda na shayi ne a bana.
Ranar Laraba 26 ga watan Afirilu, Chelsea za ta karbi bakuncin Brentford a gasar Premier League, sannan ta ziyarci Arsenal ranar Talata 2 ga watan Mayu.
Real Madrid mai maki 62 ta biyu a teburin La Liga za ta karbi bakuncin Celta Vigo ranar Asabar 22 ga watan Afirilu, sannan ta je gidan Girona ranar Talata 25 ga watan Afirilu.