An sallami koci 12 a Premier League kawo yanzu a bana

Premier Coaches sack

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Kawo yanzu masu horar da tamaula 12 aka kora a Premier League ta bana, wadda saura wasa tara-tara a kammala wasanni.

Ranar Lahadi 2 ga watan Afirilu, Leicester ta sanar da korar Brendan Rodgers, da yamma Chelsea ta sanar ta sallami Graham Potter.

Mohammed Abdu ya hada rahoto kan kociyoyin da aka kora a Premier: a 2022/23:

Scott Parker, Bournemouth,

Scott Parker

Asalin hoton, Getty Images

Bournemouth ce ta fara korar Scot Parker ranar 30 ga watan Agusta, bayan da Liverpool ta doke su 9-0 a gasar Premier League.

Sabuwar kungiyar da ta hau Premier daga Championship, wadda Parker ya sa ran za a fitar da kudi don sayo karin sabbin 'yan kwallo, amma hakan bai yi wu ba. Gary, O'Neil ne ya maye gurbinsa.

Thomas Tuchel, Chelsea

Thomas Tuchel

Asalin hoton, Getty Images

Bayan da Tuchel ya ja ragamar Chelsea ta lashe UEFA Champions League a kakar 2020/21 da UEFA Super Cup da FIFA Club World Cup ia kakar, Chelsea ta sallami Tuchel ranar 7 ga watan Satumba.

An kuma sallame shi bayan da kungiyar ta yi rashin nasara da ci 1-0 a hannun Dinamo Zagreb a Champions League.

Tun kan fara kakar Chelsea ta kashe $310m wajen sayo sabbin 'yan kwallo, amma sai kungiyar ba ta taka rawar gani.

Bruno Lage, Wolverhampton Wanderers

Buruno Lage

Asalin hoton, PA Media

Ranar 2 ga watan Oktoba, Wolverhampton ta kori Bruno Lage, bayan rashin nasara da ci 2-0 a gidan West Ham United.

Tun farko Wolves ta sa kanta cikin kungiyoyin da za a yi tata burza da ita a jerin 'yan goman farko, ashe ba haka batun yake ba da ta kai ta raba gari da kociyan.

Daga baya ta nada Julen Lopetegui tsohon kociyan Sevilla da Real Madrid, wanda ya maye gurbin Lage.

Steven Gerrard, Aston Villa

Steven Gerrard

Asalin hoton, Getty Images

Aston Villa ta sa ran a kakar nan za ta iya samun gurbin gasar zakarun Turai ko a Europa ko kuma a Confrence League, bayan da ta fitar da kudi ta sayo sabbin 'yan wasa.

Sai dai Gerrard ya tafka kuskure da ya canja kyaftin din kungiyar, sannan 'yan wasa irin su Philippe Coutinho, Emiliano Buendia, Boubacar Kamara, Jacob Ramsey da Leon Bailey sun kasa nuna kwarewarsu a Premier League.

Daga nan ta kori Gerrard ta bai wa tsohon kociyan Arsenal, Unai Emery aikin.

Ralph Hasenhüttl, Southampton

Ralph Hasenhüttl

Asalin hoton, Getty Images

Southampton ta kori Hasenhüttl ranar 6 ga watan Nuwamba ta kuma nada Nathan Jones ya maye gurbinsa.

Hasenhüttl ya fara aiki da kungiyar a 2018, amma ba ta haura mataki na 11 a teburin Premier har zuwa kakar 2019-2020 kenan ba ci gaba.

An sallame shi a lokacin da ya kai kungiyar cikin 'yan ukun karshe da yin nasara uku da canjaras uku aka doke shi wasa takwas.

Frank Lampard, Everton

Frank Lampard

Asalin hoton, Getty Images

Da aka fara kakar bana Everton ta fara da taka rawar gani daga baya komai ya koma baya a kungiyar ta kasa yin abin kirki.

Kungiyar kan kasa zura kwallo a raga, sannan ba ta buga wasa mai ban sha'awa da sauran matsaloli.

Bayan wasa 20 a Premier League, Everton ta ci karawa uku da canjaras shida da rashin nasara 11 hakan ya kai kungiyar ta 19 a kasan teburi.

Hakan ya sa ta maye gurbinsa da Sean Dyche.

Jesse Marsch, Leeds

Jesse Marsch

Asalin hoton, Getty Images

Leeds United ta kori Marsch, bayan da ta yi rashin nasara a hannun Nottingham Forest 1-0, washe gari ta sanar da korar dan kasar Amurka.

Marsch wanda ya hada maki 18 ya ci wasa hudu da canjaras shida aka doke shi karo 10, hakan ya sa ta koma cikin 'yan kasan teburi.

Leeds ta sanar da nada Javi Gracia a matakin sabon kociyanta ranar 21 ga watan Fabrairu.

Nathan Jones, Southampton

Nathan Jones

Asalin hoton, Getty Images

Karo na biyu da Southampton ta kori koci a kakar nan - an sallami Jones, bayan da wasu fitattun 'yan wasan kungiyar suka yi korafi kan kociyan.

An kore shi bayan da Southampton ta yi rashin nasara a hannun Wolves da ci 2-1 duk da cewar ita ta fara cin kwallo, sannan Wolves ta karasa da 'yan wasa 10 a cikin fili.

Patrick Vieira, Crystal Palace

Patrick Vieira

Asalin hoton, Getty Images

Palace ta dora a wasanninta, bayan da ta sallami Vieira, kwana da biyu tsakani kafin ta buga wasan da Arsenal ta yi nasara 4-1 a Emirates a wasan hamayya.

Tun kan karawar Palace ta kasa cin wasa a 2023, wadda ta nada Paddy McCarthy na rikon kwarya.

Rashin kokarin kungiyar a 2023 ya sa ta fada wani hali na fuskantar nutsewa nan da nan ta kara bai wa Roy Hodgson aikin jan ragamar kungiyar.

Hodgson ya fara horar da Palace daga 2017 zuwa 2021.

Antonio Conte, Tottenham

Antonio Conte

Asalin hoton, Getty Images

Conte da Tottenham sun raba gari bayan da kociyan ya caccaki 'yan wasa da kungiyar, bayan tashi 3-3 da Southampton a Premier Leage.

Tottenham ta fara kakar bana da kafar hagu cikin 'yan hudun farko, daga baya aka yi waje da Champions League da FA Cup ba ita ta dauki Carabao Cup na bana ba.

Kungiyar wadda take ta biyar a teburi, wadda ta yi shekara 15 ba tare da daukar babban kofi ba ta nada Cristian Stellini zuwa karshen kakar bana.

Brendan Rodgers, Leicester City

Brendan Rodgers

Asalin hoton, Getty Images

Leicester City ta kori Brendan Rodgers bayan da Crystal Palace ta doke ta 2-1 a gasar Premier League ranar Asabar.

Wasa na biyar da aka doke kungiyar King Power daga shida da ta kara a bayan nan da hakan ya sa ta koma cikin 'yan karshen teburi.

Leicester City ta dauki Rodgers aiki a Fabrairun 2019, wanda ya lashe FA Cup a kungiyar a 2021.

Daga kungiyoyi tara da ke kasan karshe a babbar gasar tamaula ta Ingila, West Ham da Nottingham Forest ne kadai ba su sallami kociyansu ba.

Graham Potter, Chelsea

Graham Potter

Asalin hoton, Getty Images

Chelsea ta sallami Graham Potter, bayan wata bakwai yana jan ragamar ƙungiyar ta Stamford Bridge.

Ranar Asabar ne, Aston Villa ta doke Chelsea 2-0 a wasan mako na 29 na Gasar Premier.

Wasa na 11 da aka doke Potter a cikin karawa 31 da ya yi jagoranci tun bayan maye gurbin Thomas Tuchel a Stamford Bridge ranar 8 ga watan Satumba.

Chelsea, wadda ta kashe sama da fam miliyan 550 wajen sayo sabbin 'yan wasa, za ta ɗauki wani kocin a kakar nan.

Kociyoyin da aka kora a Premier League a 2022/23

  • Scott Parker Bournemouth 30 ga watan Agustan 2022
  • Thomas Tuchel Chelsea 7 ga watan Satumbar 2022
  • Bruno Lage Wolves 2 ga watan Oktoban 2022
  • Steven Gerrard Aston Villa 20 ga watan Oktoban 2022
  • Ralph Hasenhuttl Southampton 7 ga watan Nuwamba
  • Frank Lampard Everton 23 ga watan Janairun 2023
  • Jesse Marsch Leeds 6 ga watan Fabrairun 2023
  • Nathan Jones Southampton 12 ga watan Fabrairun 2023
  • Patrick Vieira Crystal Palace 17 ga watan Maris 2023
  • Antonio Conte Tottenham 26 ga watan Maris 2023
  • Brendan Rodgers Leicester 2 ga watan Afirilun 2023
  • Graham Potter Chelsea 2 ga watan Afirilun 2023