Yi wa doki wanka da ziyarar Malala cikin hotunan Afirka

.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Ana yiwa doki wanka da ruwan sanyi a kogin Yoff dake Kasar Senegal, don rage masa tsananin zafi a jikinsa.
An wallafa
,

Asalin hoton, LUIS TATO/AFP

Bayanan hoto, Masu rawar Ballet a lokacin bikin rawa na 'Nutcracker' a babban ɗakin tiyata na Nairobi da ke Kenya ranar Asabar.
.

Asalin hoton, LUIS TATO/AFP

Bayanan hoto, Masu kallo da dama ciki har da 'yan makaranta ne suka kalli bikin.
.

Asalin hoton, MICHELE SPATARI/AFP

Bayanan hoto, A ranar Asabar kuma masu hutu ke shaƙatawa a kan ruwa.
.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, A ranar Litinin Firaministan Tanzaniya ya shiga sahun tawagar masu nemo mutanen da ambaliyar ruwa ta yi awon gaba da su bayan zaftarewar ƙasa.
.

Asalin hoton, ROBERTA CIUCCIO/AFP

Bayanan hoto, Malala Yousafzai na gabatar da jawabi ranar Talata ya yin bukin cika shekaru 10 da mutuwar Nelson Mandela a birnin Johannesburg dake Afirika ta Kudu.
.

Asalin hoton, DEAAN VIVIER/GETTY IMAGES

Bayanan hoto, A wannan ranar masu zanga-zangar goyon bayan Falasɗinawa suka yi dandazo a gaban mutum-mutumin Nelson Mandela a birnin Pretoria
.

Asalin hoton, AHMED JALLANZO/EPA

Bayanan hoto, Ranar Laraba lokacin da 'Yan rawa suke cashewa a titunan Monrovia babban birnin Kasar Liberia, don tunawa da Ranar Kare Hakkin Yan Adam ta Duniya.
.

Asalin hoton, ANDREW ESIEBO/GETTY IMAGES

Bayanan hoto, Yara na baje-kolin rawa a bikin 'Move Africa' wanda Kendrick Lamar ya shirya a Kadsar Rwanda ranar Laraba.
.

Asalin hoton, ISLAM SAFWAT/GETTY

Bayanan hoto, Wani mai ɗaukar hoto, ya ɗauko hoton jirgin kanun kifi a Kogin Nilu dake Alkahira babban birnin ƙasar Masar a ranar Litinin.