Leicester ta barar da damar hada maki uku a kan Brentford a King Power

An wallafa

Leicester City ta shi 2-2 da Brentford a wasan makon farko a Premier League da suka fafata ranar Lahadi a King Power.

Leicester City ta fara cin kwallo ta hannun Timothy Castagne, sannan Kiernan Dewsbury-Hall ya zura na biyu a raga.

Daga baya ne Brentford ta kara sa kwazo ta farke kwallo biyu da aka zura mata ta hannun Ivan Toney da kuma Pelenda Joshua Da silva.

Brentford ta kasa doke Leicester a wasa bakwai kenan a baya da suka hadu da canjaras biyu da shan kashi a fafatawa biyar.

Rabon da Leicester City ta yi rashin nasara a hannun Bentford tun 3-1 da aka yi mata a 1953 a lokacin da suke karamar basa mai daraja ta biyu a Ingila.

Ko a kakar Premier da ta wuce Leicester City ta doke Brentford 2-1 ranar 24 ga watan Oktoba da kuma 2-1 ranar 25 ga watan Maris a King Power.

Jamie Vardy ya ci kwallo bakwai jumma a ranar fara buge Premier League, shi ne na biyu a wannan kwazon, bayan Alan Shearer da Frank Lampard da kuma Wayne Rooney da kowanne keda takwas.

To sai dai kuma Vardy, wanda aka fara karawar da shi bai samu ya zura kwallo ba a ragar Brentford a ranar ta Lahadi.

Leicester City ba ta dauki dan kwallo ba kawo yanzu - ta kuma da mai tsaron ragarta, Kasper Schmeichel wanda ya koma Nice.

Haka kuma Newcastle na son daukar James Maddison ita kuwa Chelsea so take ta sayi Fofana.