Fafutukar #MeToo bayan shekara biyar: Akwai abin da ya sauya?

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Daga Sandrine Lungumbu
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
- An wallafa
A daidai wannan lokacin shekaru biyar da suka gabata abu ne mai wahala mutum ya ce bai lura da fafutukar #MeToo da ta karade shafukan sada zumunta ba. Abin da ya samo asali daga wani sakon Tiwita ya rikide zuwa tafka muhawara kan cin zarafin mata a sassan duniya.
"Muhawarar Me Too ba ita ce ta farko ba kan batun cin zarafin mata, kuma ba ita ce ta fara yaduwa kamar wutar daji ba, kuma a sassan duniya fafutukar ta haska aikin da aka dade ana yi amma a wani yanki na duniya", inji Farfesa karen Boyle, wadda ita ce shugabar cibiyar binciken jinsi kuma malamar Jami'ar Stathclyde.
Shin ya fafutukar ta samo asali?
Fafutukar "Me Too" ta samo asali ne yayin da Tarana Burke wata mai fafutuka wadda ta yi amfani da kalaman Me Too a 2006 domin jan hankulan jama'a kan matsalar muzgunawa mata.
Shekaru 11 bayan lokacin a 2017, fafutukar ta bayyana yayin da Alyssa Milano, wata 'yar fim Ba'Amurkiya ta wallafa sakon Tiwita tana kira ga mata su bayyana ra'ayinsu kan batutuwan cin zarafin mata da na fyade.
Milano ce mace ta farko da ta zargi attajirin mai hada fim Harvey Weinstein da cin zarafinta da yi ma ta fyade.
A ranar da ta wallafa sakon nata, 15 ga watan Oktoba, an yi amfani da kalaman "Me Too" fiye da sau 200,000 a shafukan sada zumunta, kuma zuwa kashegari a yada su fiye da sau 500,000.
#MeToo ya bazu zuwa kasashe fiye da 85 da kuma harsuna masu yawa.

Asalin hoton, Reuters
Lallai wannan fafutukar ta samo asali ne a Amurka, amma tasirinta ya zagaya duniya.
Ga Farfesa Boyle, abu mafi muhimmanci shi ne rarrabe hayaniyar da aka yi ta "Me Too" da ainihin fafutukar neman gyara.
"Na kan bambanta Me Too a matsayin fafutuka mai zaman kanta da kuma jan hankalin da aka rika yi a shafukan sada zumunta na takaitaccen lokaci. Ina ganin har yanzu fafutukar na kara karfi"
Tasirin fafutukar #MeToo a fadin duniya
A 2015 Juliana de faria, wata wadda ta assasa kungiyar "Think Olga" ta kaddamar da wata fafutuka mai suna #MeuPrimeiroAssedio ko kuma "Cin Zarafina na Farko."
Cikin 'ya kwanaki sai aka rika yada sakon cikin dubban sakonni a Tiwita da ke bayyana yadda ake muzgunawa mata da yi musu fyade a Brazil.
Ba da jimawa ba sai sakon ya bazu zuwa dukkan kasashen Lain Amurka wanda ada Sfaniyanci ake kira #MiPrimerAcoso.

Asalin hoton, Getty Images
Cikin 'yan shekarun nan an ga misalai masu yawa daga sassan duniya da suka taimakawa batun ya ci gaba da yaduwa a kasashe kamar China da Birtaniya da Indiya.
A Indiya, akwai kiraye-kiraye da ake yi na korar daraktan fina-finan Bollywood Sajid Khan daga taka rawa a shirin talabijin din nan Bigg Boss mai matukar farin jini.
Wannan matakin ya biyo bayan zargi da wasu mata takwas ke yi masa na fyade da cin zarafinsu shekaru hudu da suka gabata.
Ya musanta aikata wani laifi kuma kawo yanzu ba a gurfanar da shi a gaban shari'a ba.

A 2018, fafutukar #MeToo ta bazu a cikin China. Xianzi - wacce ainihin sunanta Zhou Xiaoxuan, na cikin mata masu yawa da suka fara bayyana yadda aka ci zarafinsu ko aka yi musu fyade.
Ta wallafa wani labari mai kalamai 3,000 wanda a ciki ta zargi Zhu Jun - wani shahararren mai gabatarwa a tashar talabijin na China CCTV da yayi ma ta fyade a 2014 yayin da ta ziyarci dakinsa domin ta sa damar yin hira da shi.
An yi watsi da karar ta a bara saboda rashin isassu hujjoji, sai dai ta kafe, tana cewa ba za ta mika wuya ba har sai an yi ma ta adalci.

A watan Mayu, daruruwan mutane sun bazama zuwa titunan kasar nepal suna neman a yi sauyi ga dokokin kasar kan bayyana abin da ake nufi da fyade bayan da wata mai tallan kayan kawa ta walafa wasu jerin bidiyo a TikTok tana cewa an yi ma ta fyade tun tana mai shekara 16 da haihuwa.

A kasar Iran kuwa, zanga-zanga ta barke bayan da aka kashe Mahsa Amini, wata 'yar kabilar Kurdawa mai shekara 22 bayan da 'yan Hizban kasar suka tsare ta na wani lokaci.
An dai kama Mahsa Aini ne saboda ba ta sanya dan kwali a kanta ba.
Abin da ya biyo bayan fafutukar #MeToo

Asalin hoton, Getty Images
Bayan shekara biyar, daya daga cikin nasarorin da masu fafutukar suka samu shi ne yadda aka fara amincewa ana yin muhawara kan tasirin cin zarafin mata.
Farfesa Boyle na ganin koma bayan da aka samu a fafutukar MeToo saboda ba a cika amincewa da bayana da mata ke yi ba ne.
Mene ne ke gaba ga fafutukar #MeToo?

Asalin hoton, Getty Images
Farfesa Boyle ta ce yaduwa kamar wutar daji da fafutukar #MeToo ta yi ta haifar da wata dama ta musamman ta muhawara amma akwai sauran aiki a gaba.
Ta ce, "A gare ni, idan ana son fafutukar #MeToo ta yadu a ko ina a duniya, tilas ne a yi sauye-sauye a wuraren aiki da makarantu da wuraren wasannin motsa jiki - a dukkan wurare. Duk da cewa wannan aikin ya dauki gomman shekaru, amma yanzu aka fara tafiyar,” in ji ta.











