Dambarwar kasafin kuɗin Najeriya da mayar da Emefiele gidan yari

An wallafa

Kungiyar NIPR ta damu kan matsayin Najeriya a idon duniya

Ƙungiyar hulda da jama'a ta NIPR a Najeriya ta buƙaci a ɗauki matakin gaggawa kan yadda mutuncin ƙasar ke zuɓewa a idon duniya saboda yadda ake gabatar da ita a matsayin matalauciya.

Ƙungiyar ta sha alwashin bin hanyoyin da suka dace domin kawo karshen lamarin, domin a cewarta Najeriya ta fi karfin matsayin da duniya ta ajiye ta a yanzu.

NIPR ta ce bayanan da ake yaɗawa kan talauci da aikata rashawa da ma sauran dabi'u marasa kyau a Najeriya, babu hakikanin gaskiya a ciki.

Dakta Sule Ya'u Sule, ɗan kwamitin koli ne na kasa a ƙungiyar, kuma babban malami a jami'ar Bayero ta Kano, dake cewa wasu tsiraru ne ke yaɗa wannan manufa.

Dakta Sule ya kuma yi bayanin ɓangarorin da wannan lamari ya shafa, lamarin da ya ce ya yi nisa wajen zubar da mutumcin Najeriyar a idon duniya.

Sojoji sun kashe manyan kwamandojin Boko Haram a Najeriya da wasu 'yan bindiga a Nijar.

Rundunar sojin sama ta Najeriya ta kai hare-haren ne kan tarin ‘yan ta’adda a wani kebabben wuri da ake kira Tagaushe a tsaunin Mandara da ke kusa da jihar Borno

Ta ce al'amarin ya faru ne a ranar 24 ga watan Nuwamba a garin Tagaushe.

Kakakin rundunar sojin Sama na Nijeriya, Air Commodore Edward Gabkwet ya shaida wa BBC cewa hoton bidiyo ya nuna cewa ‘yan ta’addan da yawansu ya zarce 100 na taruwa a wurin domin su gudanar da wani taro ko shirya yadda za su kai wani babban hari:

“An gansu sun taru a wuri guda, akwai gidaje kamar guda uku ko hudu, ba mu san abinda ya kai su wurin ba, ko sun je su yi taro ne ko sun je su yi shaye- shayensu ne ba bu wanda ya sani, amma su na rike da bindigogi kuma akwai manyan motocinsu guda uku kuma sun cika a ciki”

Rundunar sojin sama wadda ta kai hare -haren karkashin shirin Operation hadarin daji ta ce hare haren sun rutsa da wasu manyan kwamandojin Boko Haram

“An Kashe Abu Asad wanda ke aiki tare da Ali Ngulde wanda jigo ne a kungiyar Boko Haram bangaren Shekau. Akwai wasu manyan 'yan ta’adda da suka hada da Ibrahim Nakeeb da Mujaheed Dimtu da Mustafa Munzir da sauran mayaka da dama da aka kashe a hare haren ta sama” in ji shi.

Tafiyar Tinubu Dubai domin taron sauyin yanayi

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya bar ƙasar a ranar Laraba zuwa birnin Dubai na Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa domin halartar taron sauyin yanayi na COP28.

Wata sanarwa da ta fito daga hannun mai taimaka wa shugaban ƙasar kan hulɗa da jama'a, Ajuri Ngelale, ranar Talata, ta ce Tinubu zai gabatar da jawabi a taron wanda zai gudana tsakanin ranakun 1 da 2 ga watan Disamba.

Bayanin da shugaba Tinubu zai gabatar lokacin taron zai mayar da hankali ne kan matsayar Najeriya game da sauyin yanayi, musamman abin da ya shafi amfani da makamashi maras gurɓata muhalli da kuma samar da kuɗi kan ayyukan daƙile ɗumamar yanayi.

Ana sa ran kuma shugaban na Najeriya zai yi amfani da damar wajen neman ƙasashen da suka ci gaba da su ƙara tallafa wa ƙasashe masu tasowa wajen yaƙi da sauyin yanayi.

An sake mayar da Emefiele kurkuku saboda gaza cika ƙa'idar beli

Wata babbar kotun tarayya da ke zaman ta a Abuja, ta ɗage shari'ar da ake yi wa tsohon gwamnan babban bankin ƙasar (CBN) zuwa watan Janairun shekara ta 2024, yayin da zai ci gaba da zama a gidan yari har sai ya cika ƙa'idar belinsa ta kuɗi naira miliyan 300.

Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa (EFCC) ce ta gurfanar da Emefiele bisa zargin sa da laifuka shida, ciki har da zargin badaƙala da kuɗi naira biliyan 1.6.

Sai dai tsohon gwamnan babban bankin ya musanta zargin.

Yanzu kotun ta ayyana 18 ga watan Janairun 2024 domin sake zama kan shari'ar.

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ne ya dakatar da Emefiele daga muƙaminsa a ranar 9 ga watan Yuli bayan "wani bincike da ake yi da kuma shirin sake fasalin ɓangaren kuɗi na ƙasar.

Bayanan Tinubu kan kasafin kuɗin Najeriya

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gabatar da kudurin kasafin kudinsa na farko ga zaman hadin gwiwar Majalisun Najeriya.

Kasafin kudin na 2024, wanda ya kunshi sama da naira tirliyan 27.5 zai fi mayar da hankali wajen karfafa tsaron kasa da samar da aikin yi da harkokin zuba jari da rage fatara a tsakanin al’umma.

Shugaba Bola Tinubu ya ce an tsara kasafin kudin na shekara mai zuwa ne bisa hasashen sayar da gangar man fetur daya a kan dala 77.96, da hako kiyasin ganga miliyan 1.78 ta man fetur a kullum. Sannan da dalar Amurka daya a kan canjin naira 750.

Kasafin kudin ya yi kudurin kashe naira tirliyan 9.92 a bangaren ayyukan yau da kullum. Sai kuma naira tirliyan 8.25 wajen biyan bashi, yayin da manyan ayyuka za su samu naira tirliyan 8.7.

Fankon kundin kasafin kuɗi Tinubu ya ba mu — Ƴan Majalisa

Bikin gabatar da kasafin kudin a Najeriya da shugaban kasar ya yi ga majalisar dokoki ya bar baya da kura, inda wasu `yan majalisar ke zargin cewa shugaban kasar ya yaudare su inda suka ce ya mika musu kundin kudurin kasafin kudin 2024 na bogi.

A ranar Laraba ne shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gabatar da kudurin kasafin kudinsa na farko ga zaman hadin gwiwar Majalisun Najeriya.

Shugaba Bola Tinubu ya ce an tsara kasafin kudin na shekara mai zuwa ne bisa hasashen sayar da gangar man fetur daya a kan dala 77.96, da hako kiyasin ganga miliyan 1.78 ta man fetur a kullum. Sannan da dalar Amurka daya a kan canjin naira 750.

Kasafin kudin ya yi kudurin kashe naira tirliyan 9.92 a bangaren ayyukan yau da kullum. Sai kuma naira tirliyan 8.25 wajen biyan bashi, yayin da manyan ayyuka za su samu naira tirliyan 8.7.

Sai dai ƴan majalisar sun ce "babu komai a cikin wani dan akwatin da shugaban kasar ya rusuna ya ajiye a gaban zauren majalisar."

Hon Yusuf Shitu Galambi, dan majalisar wakilan Najeriya, ya shaida wa BBC cewa ko shakka babu shugaban kasa ya karanta musu jawabinsa na kasafin kudi, amma maganar kundi na kasafin kudin ba su ganshi ba.