Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ba na damuwa da masu suka ta - Iwobi
Dan kwallon Najeriya, Alex Iwobi ya ce watsi da ya yi da sauraron masu sukarsa ya taimaka masa komawa kan ganiya a Everton.
Dan wasan mai shekara 26 ya yi fama da rashin kwazo da ta kai ya shiga kunci a Merseyside tun bayan da ya koma Everton daga Arsenal a 2019.
To sai dai yanzu dan wasan ya zama kashin bayan Everton karkashin Frank Lampard a kakar bana, wanda ya nuna kansa a raba tamaula da murza leda.
''A baya can na kan saurari batutuwan da mutane ke suka ta, ''Kamar yadda Iwobi ya sanar da BBC.
''Sai dai a wannan shekarun, zuciyata kadai nake saurare, idan na san ban yi abin da ya kamata ba.''
Iwobi ya fara daga makarantar koyon tamaula ta Arsenal da cin kwallo 15 a wasa 149 a Gunners.
Dan wasan bai taka rawar gani a kakar da ya fara tamaula a Everton ba, karkashin Marco Silva da Carlo Ancelotti da kuma Rafael Benitez.
Tsohon wanda ya wakilci Ingila ya ce yana jin dadi da ake sa shi wasa a gurbi daban-daban a yanzu haka, ya kara da cewar yanzu ne yake jin dadin tamaula tun bayan shekara biyu.