PSG za ta sayar da ko dai Messi ko Mbappe ko kuma Neymar

An wallafa

Manchester City na fatan daukar dan wasan Brighton, Alexis Mac Allister, mai shekara 24 a karshen kakar bana. (Star)

Fatan da Liverpool ke yi na son daukar dan wasan Borussia Dortmund, Jude Bellingham zai iya cin karo da cikas idan ba ta samu gurbin buga Champions League a badi ba. (CaughtOffside)

Inter Milan na neman fam miliyan 62 zuwa 66 kafin ta sayar da Nicolo Barella, wanda ake alakanta shi da zai koma Liverpool. (Calciomercato - in Italian)

Watakila Inter Milan ta sayar da Marcelo Brozovic a karshen kakar nan, bayan da Barcelona da Chelsea da Real Madrid ke son yin zawarcin dan kwallon mai shekara 30.. (Gazzetta dello Sport - in Italian)

Watakila Paris St-Germain ta sayar da ko dai Lionel Messi ko Kylian Mbappe ko kuma Neymar a karshen kakar nan, bayan da kungiyar ke fatan daidaita kashe kudi daidai samu kamar yadda Uefa ta bukara, wato Uefa financial fair play. (Times - subscription required)

AC Milan ta yi wa kungiyoyin Premier League tayin Olivier Giroud, wanda ake cewa watakila ya koma West Ham ko Fulham ko Crystal Palace ko kuma Brentford. (Sun)

Arsenal ta bi sawun Manchester United iwajen zawarcin dan wasan Celta Vigo, Gabri Veiga, 20. (AS, via Sun)

Manchester United na shirin taya mai tsaron baya na Bayer Leverkusen, Deremie Frimpong, 22. (Football Insider)

Chelsea za ta bar matashin dan wasan Brazil, mai shekara 18, Andrey Santos ya buga wasannin aro a Vasco da Gama, bayan batun zuwa Palmeiras ya bi ruwa (Fabrizio Romano)

Everton da Leicester da Liverpool da Newcastle da Tottenham da West Ham da kuma Wolves na bibiyar dan kwallon Berlin, Rani Khedira, 29. (90min)

Watakila Newcastle ta yi zawarcin dan wasan Bristol City, Alex Scott, 19. (Sun)

Barcelona da Real Madrid sun sake komawa zawarcin dan wasan Bayer Leverkusen, Florian Wirtz, wanda kwanan nan ya koma wasa, bayan jinya mai tsawo. (Fijaches - in Spanish)

Burnley na son mallakar Ian Maatsen, wanda ke yi mata wasannin aro daga Chelsea a kakar nan a Turf Moor. (Sun)

Chelsea da Barcelona da Real Madrid na son daukar dan wasan Inter Milan, Marcelo Brozovic, 30. (La Gazzetta dello Sport - in Italian)

Gareth Southgate na daf da gayyatar golan Sunderland, Anthony Patterson, zuwa tawagar Ingila domin buga wasan neman shiga gasar Euro 2024 da za ta buga a watan gobe. (Sun)