Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Lafiya Zinariya: Abin da ya kamata macen da ta fara jinin haila ta sani
Danna hoton da ke sama domin sauraren shirin:
Akwai muhimman abubuwa da suka kamata ‘yan matan da suka fara tasawa su sani gabanin su fara jinin al’ada, a cewar likitoci.
Wasu daga ciki su ne samun bayanai kan shi kanshi jinin haila.
Haka kuma matakin da ya kamata ta dauka a karon farko da za ta fara ganin jinin da kuma yadda ya kamata ta dinga tsaftace jikinta a yayin jinin al’adar.
Jinin da ke zuwa wata-wata yana cikin manyan alamu na nuna cewa yarinya ta balaga, kuma ta shiga shekarun daukar ciki.
Masana a fannin kiwon lafiya sun jaddada muhimmancin cewa iyaye mata su ja ‘ya’yansu mata a jika tare da taimaka musu a lokacin jinin haila.
Wwasu 'yan mata kan samu kansu cikin wani hali, musamman ma wadanda basu da masaniya ko cikakken bayani a kan jinin wata-watan.
Wasu matan na gamuwa da ciwon mara ko rashin audugar da ya kamata su yi amfani da shi a lokacin jinin.
Wannan matsala ta kan hana ‘yan mata da dama zuwa makaranta da kuma tafiyar da ayyukansu na yau da kullum kamar yadda ya kamata.