United ta amince ta biya fan miliyan 70 don ɗaukar Casemiro daga Real

Casemiro

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ɗan wasan Brazil ɗin mai shekara 30 ya kasance a Real tun 2013, inda ya ci kofin gasar La Liga uku da na Zakarun Turai ta Champions Leagues biyar
An wallafa

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester United ta ƙulla yarjejeniya da Real Madrid don ɗaukar ɗan wasan tsakiyarta Casemiro kan fan miliyan 70.

Ɗan wasan Brazil ɗin mai shekara 30 ya kasance a Real tun 2013, inda ya ci kofin gasar La Liga uku da na Zakarun Turai ta Champions Leagues biyar.

Za a fara biyan kuɗi fan miliyan 60 da kuma miliyan 10 na tsarabe-tsarabe, yayin da Casemiro zai saka hannu kan kwantaragin shekaera huɗu tare da zaɓin tsawaita shi da shekara ɗaya.

United tana ƙasan teburi a gasar Premier League kuma za ta fafata da Liverpool a ranar Litinin.

Casemiro na gab da zama ɗaya daga cikin 'yan wasan United da suka fi kowa albashi idan ya kammala komawa ƙungiyar, inda zai zama mutum na huɗu da United ta ɗauka bayan Christian Eriksen, da Tyrell Malacia, da Lisandro Martinez.

Bayan an kasa cimma yarjejeniya ɗaukar Adrien Rabiot daga Juventus, United ta mayar da hankali kan Casemiro a yunƙurin da take yi na gyara matsalolin da take fuskanta a tsakiyar sabon mai horarwa Erik ten Hag.

Da alama ɗaukar Casemiro na nufin United za ta katse neman da take yi wa ɗan wasan tsakiyar Barcelona Frenkie de Jong.

Dan wasan Brazil ya yi atisaye da Madrid ranar Juma’a, sai dai da alama ba zai samu buga wasan na Liverpool ba a ranar Litinin saboda ba a kammala cinikin nasa a kan kari ba.