Rooney ya bayyana burinsa na zama kocin Man United

Wayne Rooney

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Wayne Rooney ya ce yana da niyyar komawa aiki cikin gaggawa a yunkurin da ya ke yi na ya cika burinsa na zama kocin Manchester United ko Everton.

Ƙungiyar Birmingham ta gasar Championship ta kori tsohon dan wasan na United da Everton a watan Janairu bayan ya shafe kwanaki 83 yana horaswa.

A baya Rooney ya taba horar da Derby County da kuma DC United da ke gasar MLS ta Amurka.

Da yake magana a lokacin da yake aiki a matsayin masani kan wasan da United ta buga a gasar FA Cup a Nottingham Forest, ya ce: "Ina so in dawo aiki domin tabbatar da cewa nan da shekaru 10 masu zuwa ina fatan samun daman kasancewa a ɗaya daga cikin manyan kungiyoyin da na yi wasa a cikinsu."

Ya ƙara da cewa "Horas da Manchester United ko Everton ne babban burinsa, wadan nan manyan ayyuka sune inda kowa ke son zuwa," in ji tsohon kyaftin din Ingilan.

An naɗa Rooney a matsayin kocin Birmingham a ranar 11 ga Oktoba, bayan yanke shawara mai cike da ce-ce-ku-ce na korar John Eustace a lokacin da ƙungiyar ke mataki na shida a gasar Championship.

A ƙarƙashin tsohon ɗan wasan, sun yi rashin nasara a wasanni tara daga cikin 15 kuma sun koma matsayi na 20 a kan teburi.

An kori Rooney bayan rashin nasara da ci 3-0 a Leeds United ranar 2 ga watan Janairu.