Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Shin Isra'ila na samun nasara a ƙoƙarinta na kawar da Hamas?
Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce burin Isra'ila a Gaza shi ne "kawar da ƙungiyar Hamas da mayaƙanta" - kuma ya sha nanata hakan a kodayaushe.
Bayan kusan wata biyar ana gwabza faɗa, da kuma kashe Falasɗinawa kimanin 30,000 a cewar ma'aikatar lafiya ƙarƙashin jagorancin Hamas, Isra'ila ta ce tana samun gagarumin nasara, don haka za ta ci gaba da faɗa har sai ta kai ga nasara a ƙarshe.
Sai dai Hamas ƙungiya ce mai iko ba wai na soji kaɗai ba - Ita ƙungiya ce ta siyasa, mai aƙida da kuma zamantakewa. Shin burin Isra'ila na kawo ƙarshen ƙungiyar baki-ɗaya zai iya yiwuwa?
Me yake faruwa a fagen daga?
Isra'ila ta ce ta ruguza rundunonin Hamas 18 cikin 24 da ke Gaza, kuma ta tarwatsa ɗaukacin tsarin sojin Hamas da ke arewacin zirin Gaza.
Rundunar tsaron Isra'ila (IDF) ta ce Hamas na da mayaƙa aƙalla 30,000 lokacin da suka ƙaddamar da farmaki kan Isra'ila ranar 7 ga watan Oktoba, tare da kashe mutum 1,200 da kuma yin garkuwa da 250.
IDF ta yi iƙirarin cewa ta kashe mayaƙa 13,000 kuma a farkon watan Fabarairu, Mista Netanyahu ya ce sojojin Isra'ila sun kashe tare da jikkatawa da kuma kama ƴan ta'adda sama da 20,000 - sama da rabin mayaƙan da Hamas take da su.
BBC ba ta kai ga tabbatar da waɗannan alkaluma ba, kuma IDF ba ta mayar da martani kan tsare-tsarenta ba. Waɗannan alƙaluma da ke fitowa daga Isra'ila da Gaza na saɓani da juna, inda ma'aikatar lafiya a can ta bayyana cewa akwai maza matasa ciki har da fararen hula cikin mutum 9,000 da suka mutu a Gaza.
Ofishin siyasa na Hamas ya faɗa wa BBC cewa sun yi watsi da iƙirarin Isra'ila, kuma sojojinta na ci gaba da aiki da ƙarfinsu a dukkanin yankunan Gaza.
A daya gefe, wani rahoton jaridar Haaretz na Isra'ila ya ce Hamas ta fara dawo da wasu rundunoninta.
"Hamas za ta iya ɗaukan sabbin mayaƙa cikin sauƙi don haka ba shi ne abun da muke dubawa ba," in ji Jeremy Binnie, wakilin jaridar Defence Weekly a Gabas Ta Tsakiya.
Wani kanar ɗin sojan Isra'ila da ya yi ritaya, Miri Eisin na cibiyar yaƙi da ta'addanci a jami'ar Reichman a Isra'ila, ya ce sojojin Isra'ila sun kashe kwamandojin soja da gano makamai, kuma suna ci gaba da bin diddigin hanyoyin ƙarƙashin ƙasa na ƙungiyar Hamas.
Duk da zarge-zargen da ake yi wa Isra'ila na karya dokokin ƙasa da ƙasa da kuma shari'ar kisan kare dangi da kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ke yi wa Isra'ila - wanda Isra'ilar ta musanta - Mr Netanyahu ya haƙiƙance cewa Isra'ila za ta ci gaba da faɗa domin kawo ƙarshen sauran mayaƙan Hamas.
Shin za a iya kawar da aƙida?
Ƙasashen yamma na ganin Hamas a matsayin ƙungiyar ta'addanci, inda da yawa ke nuni da cewa shugabanninta na ci gaba da kiran ruguza Isra'ila, amma a matsayin jajirtacciyar ƙungiya a Ƙasashen Larabawa.
Hamas ta mulki Zirin Gaza tun 2007 bayan samun nasara a zaɓen 2006 da kuma tilasta wa ƙungiyar Fatah da suke gaba ficewa.
Isra'ila ta toshe hanyoyin shiga Zirin Gaza har ma da Masar tun wancan lokaci - inda ƙasashen biyu suka ce sun yi haka ne saboda tsaro.
Ƙungiyoyin Falasɗinawa sun harba dubban rokoki daga Gaza zuwa cikin Isra'ila a cikin shekara 20 da suka wuce - wasu lokutan suna haka ne don adawa da cin zarafin da sojojin Isra'ila ke yi a Gaɓar Yamma ko kuma Gabashin Birnin Ƙudus da suka mamaye.
Hamas ba ƙungiya ce ta sojoji kaɗai ba, ko kuma ta siyasa - ƙungiya ce mai aƙida," in ji Hugh Lovatt, wani babban ƙwararre a Gabas Ta Tsakiya a cibiyar Tarayyar Turai kan harkokin waje.
"Ba za a iya kawo ƙarshen wannan aƙida ba, Isra'ila ba za ta iya haka ba ko da ƙarfin soji," in ji shi.
Dr Amjad Abu El Ezz, malami a sashen harkokin ƙasashen waje a jami'ar Arab American University da ke Gaɓar Yamma, ya ce Falasɗinawa da dama na goyon Hamas saboda ba sa ganin makoma mai kyau.
Firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu, ya nuna adawa da batun kirkirar ƙasar Falasɗinawa a ɗaukacin rayuwarsa. Ya ce batun tsaro shi ya sa ya ki aminta da hakan, da kuma ƙasa amincewa da Isra'ila da Hamas ta yi.
Sai dai mutane da dama cikin jam'iyyarsa da kuma masu tsassauran ra'ayi da ke cikin gwamnati na kallon Gaɓar Yamma da Zirin Gaza a matsayin mallakin Isra'ila.
A bara, gwamnatin Isra'ila ta amince da gina gidaje da dama a wuraren da Isra'ilawa ke zama a Gaɓar Yamma, a cewar ƙungiyar gwagwarmayar Isra'ila ta Peace Now.
A 2023, sojojn Isra'ila da ƴan kama wuri zauna sun kashe aƙalla Falasɗinawa 507 aka kashe a Gaɓar Yamma, ciki har da yara 81, abin da ya sa shekarar ta zama mafi muni ga Falasɗinawa tun bayan da Ofishin Majalisar Ɗinkin Duniya mai kula da Jin Kai ya fara ɗaukar alkaluman waɗandan lamarin ke rutsawa da su a 2005.
MDD ta ce Isra'ila 36 ne rikici ya rutsa da su a hare-haren da Falasɗinawa suka kai Gaɓar Yamma.
Ƙari, akwai fushi a cikin wata hukumar Falasɗinawa, wanda Fatah ke da rinjaye da kuma ke mulkar wani ɓangare na Gaɓar Yamma. Falasɗinawa da dama na ganin hukumar a matsayin mai cike da cin hanci wadda ba ta karfin tunƙarar Isra'ila bayan mamayar da suka yi.
Kafin ranar 7 ga watan Oktoba, Falasɗinawa da ke rayuwa a Gaza cikin kunci, sun ce suna ji kamar suna zaune cikin kurkuru, in ji Dr Abu El Ezz, inda ya ƙara da cewa waɗanda ke zauney a Gaɓar Yamma sun fusata da hare-haren Yahudawa ƴan kama wuri zauna, kwace musu wuri da kuma rashin ayyukan yi.
Ya bayyana cewa al'ummar Falasɗinawa na da matasa da yawa, kuma sakamakon rashin zaman lafiya, ya sa wasu ɓangarori ba su da wani abu da yaɗa wa matasan Falasɗianwa".
"Muddin mamayar Isra'ila ba ta zo karshe ba, muddin akwai kashe-kashe, to mutane da dama za su bi abin da Hamas ke cewa - saboda suna neman mafita," in ji shi.
Wane irin goyon baya Hamas ke samu?
Duk da irin wahalhalu da Falasɗinawa da ke Gaza ke ciki tun bayan harin ranar 7 ga Oktoba, wata kuri'ar jin ra'ayin jama'a da aka yi a karshen 2023, ta nuna cewa goyon bayan da Hamas ke samu ya ƙaru tsakanin Falasɗinawa.
A Gaɓar Yamma, goyon bayan Hamas ya ƙaru daga kashi 12 a watan Satumba zuwa kashi 42 a Disamba, a cewar wani bincike kan Falasɗinawa 750 a Gaɓar Yamma da kuma 481 a Gaza.
Dr Khalil Shikaki, na cibiyar bincike da tsare-tsare ta Falasɗinawa a Gaɓar Yamma, wadda ta gudanar da kuri'ar, ya ce goyon bayan da Hamas ke samu na tashi lokacin yaƙi, sai dai wannan ya zo da mamaki.
Ya lura da cewa lokacin da aka gudanar da kuri'ar jin ra'ayin jama'a, lokacin da aka tsagaita wuta tsakanin Hamas da Isra'ila a watan Nuwamba, an saki mata da yara Falasɗinawa daga gidajen yarin Isra'ila.
Ya ce wannan ya janyo wasu na ganin cewa amfani da rikicin Hamas a matsayin hanya mai kyau wajen cimma burin Falasɗinawa.
Sai dai abin ba haka yake ba a Gaza, inda goyon bayan Hamas ya ƙaru da kaɗan, daga kashi 38 zuwa 42 - a kuri'ar da aka yi.
Mutane kalilan ne daga Gaza suke ganin Hamas ta yi daidai wajen kaddamar da hari kan Isra'ila ranar 7 ga Oktoba, inda ta samu goyon baya da kashi 57, idan aka kwatanta shi da 82 da Hamas ɗin ta samu a Gaɓar Yamma.
"Ta nuna ƙarara cewa waɗanda ke ɗanɗana kuɗarsu bayan harin Hamas su ne ke sukar ƙungiyar," in ji Dr Shikaki.
Ƴan jaridan BBC waɗanda ke aiko rahotanni daga Gaza har zuwa farkon watan Febrairu, sun lura da cewa akwai ƙaruwar fushi da kuma kin amincewa da Hamas a watannin baya-bayan nan.
Wasu ƴan Gaza da suka tattauna da su sun bayyana ɓacin-rai kan mutuwar ƴan uwansu da lalata gidajensu da sojojin Isra'ila ke yi da kuma yunwa a matsayin abubuwan da suka sa suke yin fushi da ƙungiyar.
Sun kuma bayar da rahoton cewa a yawan lokuta ƴan Gaza na nuna damuwa kan fitowa su soki Hamas.
Zamanin Sabbin mayaka?
Dr Abu El Ezz ya yi imanin cewa a yanzu matasa da yawa a Gaza na cike da "kin jin Isra'ila da kuma mamayarta".
"Ina ganin cewa matasa masu tasowa za su shiga cikin wannan ƙungiya domin ɗaukar fansa, saboda sun rasa iyalansu, sun rasa ƴaƴansu, sun rasa mahaifansu da sauransu...," in ji shi.
Sai dai Kanal Eisin ta ce buƙatar samar wa Hamas goyon baya kar ta wuce kan cimma burin soji.
Ta lura da cewa harin ranar 7 ga Oktoba ta nuna ta masu tsassauran ra'ayi ce.
Sai dai Dr Shikaki ya ce: "babbar yaƙi ba lallai ta janyo matasa su ɗauki makamai ba, idan zaman lafiya ya biyo baya."
Me ya faru washegari bayan harin Hamas?
Mr Netanyahu ya bayyana wani tsari na bayan yaƙi, inda Isra'ila za ta karɓi iko da batun tsaro a Gaza, inda Falasɗinawa waɗanda ba su da alaƙa da ƙungiyoyi da ke faɗa da Isra'ila za su tafiyar da yankin.
Kanal Eisin ta ce a kodayasuhe Hamas na da abin da za ta nuna, sai dai ta yi imanin cewa Isra'ila za ta iya shafe da yawa daga cikin mayakan ƙungiyar - da kuma rage barazanarsu.
"Idan da gaske ana son kawar da Hamas da kuma karya lagonta, to hanya ɗaya ita ce ta kirkiro da wani tsari na siyasa," in ji Mr Lovatt.
Sai dai batun samar da ƙasahe biyu a matsayin mafita na ƙasa yana dabo.
A baya-bayan nan Mr Netanyahu ya wallafa a shafinsa na X cewa "Isra'ila ba za ta yi wasa da batun karɓar iko da tsaro a ɗaukacin Gaɓar Yamma da Kogin Jordan ba - hakan kuma ya saɓa wa batun kirkiro da ƙasar Falasɗinawa".
Gwamnatin shugaba Joe Biden ta faɗa ƙarara cewa kada Isra'ila ta ci gaba da mamaya a Gaza. Ganin cewa ɓangarorin da ke faɗa ba su cimma matsaya ba, akwai barazanar cewa rikicin zai iya yaɗuwa nan gaba.
"Ban san ranar da Isra'ila za ta samu nasara za ta kasance ba," in ji Mr Binnie.
"Za su karya Hamas, sai dai abu guda shi ne ta yaya za a hana Hamas daga sake farfaɗowa bayan nan?"