Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Manyan ƙaburburan da dakarun Isra'ila suka bari bayan ficewarsu daga asibitin al-Shifa
- Marubuci, Yolande Knell
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakiliyar Gabas ta Tsakiya
- Aiko rahoto daga, Jerusalem
- Marubuci, Rushdi Abu Alouf
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakili daga Gaza
- Aiko rahoto daga, Istanbul
- An wallafa
Dakarun Isra'ila sun fice daga ginin asibitin al-Shifa na Zirin Gaza ranar 1 ga watan Afirilu, bayan hari na biyu da suka kai cikin asibitin, wanda ya girgiza Falasɗinawa a cikin wani yanayi da suka kamanta da tarkon muntuwa.
A cikin watanni takwas da aka shafe ana yaƙin, an riƙa kai hare-hare a asibitoci, inda Isra'ila ta yi iƙirarin cewa mayaƙan Hamas na ɓoyewa a ciki, zargin da ƙungiyar ta musanta.
Amma harin da ya fi ɗaukar hankali shi ne na asibitin al-Shifa, wanda ya taɓa zama cibiyar kula da lafiya mafi wadatuwar kayan aiki a Zirin Gaza.
Gwamnatin Isra'ila ta bayyana harin na mako biyu a matsayin wanda ya zama wajibi, tana mai cewa mayakan Hamas sun taru a cikin asibitin domin tsara nasu hare-haren.
Kakakin gwamnatin, Avi Hyman ya ce sun kashe ƴan ta'adda 200, tare da kama wasu 900, kuma babu farin hular da harin ya shafa.
Amma yadda ake zaƙulo ruɓaɓɓun gawarwaki daga cikin ɓaraguzai a al-Shifa, wani abu ne mai janyo shakku a kan iƙirarin gwamnatin Isra'ila.
A makonnin bayan nan an gano wasu manyan kaburbura huɗu a yankin, kuma tawagar Falasɗinawa mai aikin zaƙulo gawarwakin ya ce an gano ɗaruruwan gawa a wajen.
Mun yi aiki tare da wani ɗan jarida a Gaza domin bibiyar yanayin da ake ciki.
Wani darakta a asibitin, Dr Mohamed Mughir, ya bayyana cewa babu dai cikakkun kayan aiki domin gudanar da bincike a kan gawarwakin, amma tawagar da ke aikin zaƙulo su tana amfani da hotunan da aka ɗauka na gawarwakin wajen gabatar da hujjar aikata kisa kan fararen hula, kuma hotunn sun riƙa nuna harbi a kan jikin gawarwakin da kuma alamun an azabtar da su kafin mutuwa.
Kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana matuƙar damuwa a kan gano manyan kaburbura a asibitin al-shifa da kuma na Nasser da ke kudancin Gaza. Kuma kwamitin ya yi tarayya da Amurka da Tarayyar Turai wajen yin kiran a gudanar da bincike mai zaman kansa domin tabbatar da zargin da ake yiwa Isra'ilan na aikata laifin yaƙi.
Rundunar sojin Isra'ilan dai ta ce a lokacin da suka afkawa asibitin na Gaza, dakarun ta sun zaƙulo gawarwakin mutanen da Falasɗinawa suka binne tun baya, a cikin ƙaƙarin da dakarun Isra'ilan ke yi na gano wajen da Hamas ke tsare da mutane 250 da ta yi garkuwa da su bayan harin da ta kaiwa yahudawa a ranar 7 ga watan Oktoba.
Runudnar Isra'ilan ta haƙiƙance cewa ta bi ƙa'ida wajen nazari a kan gawarwakin kuma ta mayar da Yahudawan da ta gano zuwa gida.
Sai dai kuma alamu na nuna cewa, wasu daga cikin gawarwakin da aka gano daga baya a asibitin al-Shifa gawarwaki ne na marasa lafiya da ke kwance a asibitin kafin kai harin Isra'ila. Ma'aikatan lafiya kuma sun tabbatar cewa an riƙa ganin allurar ƙarin ruwa a jikin gawarwakin.
A ranar 15 ga watan Afirilu BBC ta gana da wasu maza biyu waɗanda mahaifiyar su da ta rasu bayan jinya a asibitin. Tana cikin gawarwakin da aka zaƙulo daga manyan kaburburan.
Mohammed al-Khatib, wanda ya shafe kwanaki yana neman mahaifiyar sa, Khawla ya ce “Na iso wajen nan a guje bayan samun labarun gano wani babban kabari, cikin ikon Allah mun gano gawar ta''
Walid Fatima ya ce mahaifiyarsa, Lina Abu Leila, tana cikin waɗanda aka zaƙulo daga kabarin, kuma ya iya gano ta ne saboda ciwon da take da shi a ƴan yatsun ta na ƙafa, bayan harin da dakarun Isra'ila suka kai Gaza a bara. was being treated for malnutrition and severe dehydration when she died.
A farkon harin da ta ƙaddamar asibitin, a ranar 18 ga watan Maris, rundunar sojin Isra'ila ta umarci dubban fararen hula da ke fakewa a asibitin su gaggauta ficewa domin komawa kudancin Gaza. Amma ta ce asibitin zai iya ci gaba da aikin sa. Duk da cewa mako biyu bayan umarnin, marasa lafiya 140 ne da ma'aikatan lafiya kacal suka rage a cikin asibitin.
Wakilin hukumar lafiya da duniya a yankin, Dr Rik Peeperkorn, ya ce ma'aikatn lafiya da ke asibitin sun sha wahala sosai, inda suka riƙa canza wajen zama daga lokaci zuwa lokaci, har suka kai ga zama a sashin mulki na asibitin wanda baya da kayan aikin da ake buƙata domin kula da marasa lafiya. Ya kuma tabbatar da cewa marasa lafiya 20 suka mutu.
Marasa lafiya da dama da suka tsira da rai sun shaida mana cewa an riƙa basu abinci ɗan kaɗan a zaman su asibitin. Sun kuma koka a kan ƙarancin ruwan sha da magani. Dukkan su dai sun jikkata ne saboda hare-haren Isra'ila na baya.
Mohamed al-Nadeem, wanda ke fama da matsalar shanyewar jiki ya ce “An riƙa yi mana luguden bama-bamai ba dare ba rana, ciwo ya kwantar dani ko tafiya bana iyawa. Kuma na riƙa kwana a ƙasa, babu ko mayafi.”
Rafif Doghmush, mai shekara15, kuma wanda aka yankewa ƙafafu ya ce ''Babu bandeji, kuma babu maganin kashe zafi''
Rundunar sojin Isra'ila dai ta shaidawa ƴan jarida cewa harin nata bai kashe marasa lafiya ko ma'aikacin asibitin ba.
Wani bidiyon da aka naɗa ta sama ya nuna yadda wasu Falasɗinawa ke harbin dakarun Isra'ila da bindiga daga cikin asibitin. kuma rahotanni sun ce daga baya ƴan bindigar sun laɓe a ɗakunan jinya inda suka riƙa harbin dakarun Isra'ilan.
Dakarun Isra'ila uku ne aka tabbatar an kashe a makonni biyu na wannan hari.
Duk da cewa Hamas ta musanta laɓewa a cikin asibitin, jami'an sun ce akwai mambobinsu a cikin asibitin, lamarin da ke nuni da cewa suna cikin ɗimbin mutanen da suka ɓoye a ciki.
Daga cikin mutanen da Isra'ila ta kira ƴan ta'addar da suka ɓoye a cikin asibitin har da Faiq al-Mabhouh, wanda ta ce shi ne kwamandan mayakan Hamas a asibitin, amma ofishin yaɗa labaran gwamnatin Hamas ya ce ɗansanda ne da ke aikin kai tallafi Gaza.
A cikin watan Afirilu rundunar sojin Isra'ila ta fitar da wani bidiyo da ke nuna yadda aka riƙa tambayar, Tarek Abu Shaluf, kakakin ɓangaren siysar na Hamas, wanda ta ce ta kama a cikin asibitin al-shifa.
Hamas dai ba ta tantance sunayen da dakarun Isra'ilan suka fitar ba, lamarin da ya sa ake da shakku a kan ingancin bayanin rundunar.
Duk da cewa Isra'ila ta tsaya kai da fata cewa bata kashe fararen hula ko ɗaya ba a harin nata, mun samu bayanai da ke bayar da tabbacin an kashe Falasɗinawa a lokacin harin bama-baman na Isra'ilan.
Rundunar tsaron farin kaya ta Falasdinawa ta shaida mana cew akwai sauran Falasɗinawa da ake nema har yanzu, tun bayan harin na watan Maris.
Akwai dai karo da juna a rahotannin da ake fitarwa a game da bin da ya faru a cikin asibitin al-shifa da kuma harabar sa.
Da farko dai Isra'ila ta jajirce cewa a cikin asibitin ne Hamas ke tsare da mutanen da ta yi garkuwa da su. Ta kuma wallafa wasu hotunan taswirar wajen da ke nuna hanyoyin ƙarƙashin ƙasa da ake da su a cikin asibitin, inda ta ce Hamas na amfani dasu wajen kitsa ayyukan ta.
Rundunar sojin Isra'ilan ta ce ta gano gawar biyu daga cikin Isra'ilawan da Hamas ta yi garkuwa da su, a gefen asibitin, amma bidiyon da aka naɗa a wajen bai nuna hakan ba.
Da ta koma asibitin daga baya, Rundunar Isra'ila ta fitar da hotunan kuɗi da makamai da alburusai da tace ta samu a wajen, tare da wasu takardun bayanan ƙungiyar Hamas.
Asibitin al-shifa dai ya zamu wani abin tafka muhawara game da rahoton ko Hamas na amfani da asibitoci domin ɓoye mayaƙan ta.
Hamas ta musanta fakewa cikin fararen hula, kuam ta zargi Isra'ila da aikata laifukan yaƙi, musamman ma keta haƙƙin ɗan Adam.
A watan Afirilu Majalisar Dinkin Duniya ta yi kiran a gudanar da binciken ƙeƙe-da-ƙeƙe a kan manyan kaburburan da aka gano a Gaza, kuma kakakin ta Stephane Dujarric ya ce akwai buƙatar bai wa ƴan jarida damar shiga su ganar wa idanun su abin da ya faru.
Da aka fara yaƙin dai akwai matakan da Isra'ila da Masar suka ɗauka na hana kafafen yaɗa labarai na ƙasar waje shiga domin ɗaukar rahotanni.
Masu bincike daga ƙasashen duniya basu samu damar shiga domin binciken hakiƙanin abin da ya faru ba. Lamarin da ya tilasta amfani da bayanan da kafafen yaɗa labaran cikin gida suka fitar.
Duk da cewa an rusa mafi yawan asibitin al-shifa, an fara yunƙurin fara kula da marasa lafiya a asibitin. Daga baya kuma Isra'ila ta karkata zuwa kai hre-hare a kan wasu cibiyoyin kula da lafiya da suka ce Hamas na amfani da su, musamman na Kamal Adwan da ke arewacin Gaza.