Ana farautar maharan da ake zargi da kashe mutane da wuka a Canada

An wallafa

‘Yan sanda a lardin Saskatchewan na tsakiyar ƙasar Canada na can sun dukufa ba ji ba gani wajen neman wasu mutane biyu da ake zargi da  kashe mutane aƙalla goma da kuma jikkata wasu 15 ta hanyar daba musu wuƙa.

Hukumomi sun gargadi mutanen yankin da abin ya faru da su yi taka tsan-tsan tare da sanya ido sosai a kan duk wata bakuwar fuska, su zauna a gida kuma masu ababan hawa a titi da kada su rage wa wani hanya.

Tuni dai ‘yan sanda da ke farautar wadanda ake zargi da aikata wannan ta’asa suka bayyana sunaye tare da fitar da hotunan  mutane biyun da ake zargi.

Mutanen su ne, Damien Sanderson mai shekara 31 da Myles Sanderson, mai shekara 30, wadanda suka shiga buya, kuma ‘yan sandan sun bayyana su a matsayin masu hadari  da ke dauke da makamai.

An bukaci mazauna lardin mai girman gaske da su kasance wuri ɗaya ba fita yayin da ake ci gaba da farautar mutanen, haikan.

A wani sakon tuwita, 'yan sandan sun bukaci jama’a da su yi taka tsan-tsan a duk inda suke.

Kada su bar wani bako ya shiga gidansu.

An kakkafa shingayen binciken ababan hawa, inda 'yan sanda ke binciken matafiya, sannan an yi kira ga masu ababan hawa da su guji rage hanya ga kowa.

An ayyana dokar ta-baci a wata unguwa da ke arewa maso gabashin Weldon da ke da mutane kusan 2,000.

An kuma aike da sakon gargadi ta waya ga jama'a a kan mutumin da ke da haɗari a dukkanin lardunan Saskatchewan da Manitoba da kuma Alberta - wadanda girmansu ya kai kusan rabin nahiyar Turai gaba ɗaya.

Firaministan kasar ta Canada Justin Trudeau ya bayyana harin a matsayin mai ban tsoro da takaici.

A sakon da ya sanya a shafinsa na tuwita ya ce yana tunanin wadanda suka rasa ransu da kuma wadanda aka raunata.

A wani taron manema labarai da 'yan sanda suka yi sun ce suna jin akwai karin mutanen da maharan suka raunata, wadanda suka kai kansu asibiti, inda suka bukaci mutanen da su tuntubi hukuma.

Babbar jami'ar 'yan sanda ta lardin Saskatchewan, Rhonda Blackmore, ta ce suna ganin wasu daga cikin wadanda harin ya rutsa da su maharan sun nufe su ne da niyya wasu kuma harin kan mai-uwa-da-wabi ne na maharan ya fada musu.

Jami'ar ta ce an fara yi musu waya ta gaggawa ne ta farko da misalin karfe 5:40 na kasar (11:40 agogon GMT), a babban birnin lardin, Regina, da ke da nisan kusan kilomita 280 kudu da Weldon.

Daga nan sai kuma aka rika yi musu waya kusan ba kakkautawa ana ta neman taimako

Jama'a sun ga maharan gani na karshe a Regina, a kusan lokacin cin abincin rana, a ranar Lahadi, kamar yadda bayanai suka nuna.

Mutanen da ake zargin an ce watakila suna cikin wata bakar mota ne, kirar Nissan Rogue, in ji jami'ar 'yan sandan, tana mai gargadi ga duk wanda ya gansu ya guje su, kawai ya kira lambar waya ta 911 cikin gaggawa.

Ta ce ba a san takamaimai wuri ko inda mutanen suka nufa ba, saboda haka ne suka bukaci kowa ya sa ido tare da taka tsan-tsan.