Waiwaye: Kai hari gidan yarin Kuje da kan motocin shugaban ƙasa, rasuwar shugaban OPEC

An wallafa

Ga wasu muhimman abubuwa da suka faru a wannan makon a Najeriya daga ranar Lahadi 03 ga watan Yuli zuwa Asabar 09 ga wata.

An kai wa ayarin motocin Shugaba Buhari hari

A makon da ya gabata ne Gwamnatin Najeriya ta bayyana damuwarta da bacin ranta kan wani hari da aka kai wa ayarin motocin Shugaba Muhammadu Buhari a kusa da garin Dutsinma na Jihar Katsina.

Wata sanarwa da Malam Garba Shehu, mai magana da yawun shugaban kasar ya fitar ta ce an kai harin ne kan ayarin motoci dauke da jami'an da ke wa shugaban hidima yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa Daura gabanin bikin Babbar Sallah.

Sanarwar ta kuma ce shugaban na Najeriya ba ya cikin ayarin motocin.

'Yan Bindiga sun kai hari a gidan yarin Kuje

A makon da ya gabata ne 'yan bindiga suka kai hari a gidan yarin Kuje da ke Abuja babban birnin Najeriya.

Lamarin ya faru ne a ranar Talata da daddare, inda bayanai suka ce wasu daga cikin fursunonin sun tsere.

Wani mutum da BBC ta zanta da shi ya bayyana cewa maharan sun yi ta kabbara tare da harba rokoki a cikin gidan yarin.

A cewar wani da lamarin ya faru a gabansa, 'yan bindigar sun ci karfin jami'an tsaro inda aka yi ta musayar wuta.

Babban sakataren OPEC Sanusi Barkindo ya rasu

A ranar da aka kai hari gidan yarin Kuje da kuma kai hari ga ayarin motocin shugaban ƙasa ne dai Allah Ya yi wa Babban Sakataren Kungiyar kasashen da ke da arzikin man fetur, OPEC, Dr Muhammad Sanusi Barkindo rasuwa a ranar Talata da daddare.

Rasuwarsa ta zo farat ɗaya, inda ko a ranar Talatar da rana ya kai wa Shugaba Muhammadu Buhari ziyara a fadarsa ta Aso Rock da ke Abuja, tare da tawagar shugabannin Kungiyar OPEC. 

Margayi Sanusi Barkindo na shirin sauka saga mukaminsa na sakataren OPEC bayan shafe shekaru shida a kan kujerar.

Rasuwar Nura Mustapha Waye, daraktan 'Izzar So'

A Lahadin da ta gabata ne aka yi jana'izar Nura Mustapha Waye, daraktan shirin nan mai dogon zango na 'Izzar So', wanda ake nunawa a dandalin YouTube.

Tun bayan rasuwarsa, jama'a da dama musamman abokan sana'arsa ta fim, suke ta yin alhini a shafukan sada zumunta.

Sanarwar rasuwarsa dai ta bai wa mutane da dama mamaki ganin cewa ba a san shi da wata rashin lafiya ba, kuma lafiya kalau aka rabu da shi kwana guda kafin rasuwarsa, kamar yadda makusantansa suka bayyana.

An gudanar da jana'izarsa a unguwarsu ta Goron Dutse da ke birnin Kano a arewacin Najeriya.

Wadanda aka sace a jirgin ƙasan Abuja-Kaduna sun yi kwana 100 a hannun ƴan bindiga

A ranar Larabar da ta gabata ne dai waɗanda aka sace a jirgin ƙasan Abuja-Kaduna suka yi kwana 100 a hannun ƴan bindiga.

Fiye da mutum hamsin ne, ake kyautata zaton suna hannun `yan bindigar, ciki har da mata da kananan yara, kuma tun lokacin da aka sace su mahukunta ke ikirarin daukar matakan kubutar da su amma har yanzu haƙa ba ta cimma ruwa ba.

Dangi da abokan arzikin wadanda aka sacen sun yanke shawarar gudanar da zanga-zangar lumana don jan hankalin mahukunta game da halin da `yan uwansu ke ciki.