Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Asamoah Gyan zai biya tsohuwar matarsa diyya
Asamoah Gyan zai biya diyya ga tsohuwar matarsa, bayan mutuwar aurensu, wanda akwai 'ya'ya uku a tsakani.
Wata kotu a Ghana ta umarci dan kwallon mai shekara 37, ya bai wa Gifty Gyan gidansa na Burtaniya da na Ghana da gidan mai da kuma motoci guda biyu.
Shekara uku suka yi kan shari'ar a kotu, bayan rabuwar auren, wanda tsohon kyaftin din na Ghana ya yi zargin cewa tana bin maza, sannan 'ya'ya ukun da ta haifa, ba nasa ba ne.
Da aka yi gwajin kwayayen halitta, an gano cewar shi ne mahaifin yaran uku.
A ranar Talata kotun ta yanke hukunci, inda ta umarci tsohon dan wasan Udinese din da Rennes da Sunderland, ya biya kudin Ghana, cedi 25,000 kowanne wata a matsayin kudin kula da yaran.
Tun farko, sun rabu, ba sa zaune gida daya, kotu kuma ta haramta auren nasu, sakamakon korafin da Asamoah Gyan.
Kotun ta ce Gifty Gyan ta bayar da gagarumar gudunmuwa wajen tara dukiyar da ya mallaka, saboda ita ce ta dinga kula da yaransu a lokacin da yake yawan taka leda.
Tun kafin su yi aure a tsakaninsu shekara 10 baya sun haifi yara guda biyu.
Gyan ya sanar da yin ritaya daga taka leda a watan Yuni, bayan ya ci wa tawagar Ghana kwallo 51 a wasa 109.
BBC ta tuntubi tsohon dan wasan na Ghana ta hannun wakilansa, amma bai ce komai ba.