Farashin da aka siye ni a Arsenal ake kallo ba kwallona ba - Pepe

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Nicolas Pepe ya ce ya ɗauki ƙaddara kan barin Arsenal da ya yi, amma ya ce magoya bayan Arsenal sun rika kwatanta ƙoƙarinsa da kudin da aka saye shi, wanda kuma ba daidai ba ne haka.

Da mutane sun ambaci sunan ɗan wasan mai shekara 29, sai a tuna da kudin da aka saye shi a matsayin wanda ya fi kowa tsada fan miliyan 72 a tarihin Arsenal da ta saya daga Lille.

Ya amince cewa ya yi ta fama da tashi fadi domin kwallo ta karbe shi a ƙungiyar.

"Ba sauki kwata-kwata, magoya baya ba su ji dadin kokarina ba a kungiyar, kamar yadda ya shaida wa BBC.

"Lokacin da na fara kwallo a ƙungiyar magoya bayan ba sa min hukunci da kokarina, kawai kudin da aka saye ni suke kallo. Amma dai na yi abin da ya dace a Arsenal. Ba na nadama kan hakan.

"Kudin da aka saye ni ne sun yi yawa, magoya baya na tsammanin duk wasa sai na ci kwallo."

Arsenal da suka ɗauki Pepe a 2019 bayan rawar da ya taka a kakar a Lille, lokacin da ya ci kwallo 23 ya kuma bayar da 12 aka ci, amma bayan ya zo Ingila sai ya sauya kwata-kwata.

Ya buga wasansa na ƙarshe a Arsenal a 2022, bayan wata dogon zama da ya yi a Nice a matsayin aro, yanzu dai ba shi da kulob, tun da ya bar ƙungiyar Trabzonspor ta Turkiyya.