Messi zai yi kan-kan-kan da Matthaus a yawan buga Kofin Duniya

Asalin hoton, Getty Images
Argentina za ta fafata da Croatia ranar Talata a karawar daf da karshe a Gasar Kofin Duniya da ake yi a Qatar.
kyaftin din Argentina, Lionel Messi, mai shekara 35 mai buga gasar Kofin Duniya karo na biyar zai yi bajinta a wasan da za a yi a filin Lusai.
Dan kwallon da ke taka leda a Paris St Germain zai buga wasa na 25 a Gasar Kofin Duniya, kenan zai yi kan-kan-kan da Lothar Matthaus na Jamus.
Haka kuma ya yi kan-kan-kan da Gabriel Batistuta a yawan ci wa Argentina kwallaye a Kofin Duniya masu goma-goma a raga.
Yana kuma fatan yin kan-kan-kan da Diego Maradona mai tarihin bayar da kwallo sau takwas ana zurawa a raga, bayan da Messi keda bakwai.
Matthaus ya buga wa tawagar Jamus dukkan Gasar Cin Kofin Duniya tun daga 1982 zuwa 1998.
Kenan Messi zai kafa tarihin yawan buga wasanni a Gasar Kofin Duniya ko dai a neman na uku idan Croatia ta yi nasara ko a wasan karshe idan Argentina ta kai zagayen karshe.
Messi ya kusan daukar kofin duniya a 2014, inda suka buga wasan karshe da Jamus ta yi nasara da ci 1-0 a karin lokaci.
Kawo yanzu Messi ya ci kwallo 10 a fafatawa 24 da ya buga a dukkan kofin duniya da ya halarta, yana cikin na takwas a jerin wadanda suka ci kwallaye da yawa a Gasar Kofin Duniya.
Miroslav Klose shi ne kan gaba a yawan cin kwallaye a karawa 24 da ya yi Gasar Kofin Duniya, wanda yake da 16 a raga.
Argentina tana da Kofin Duniya biyu, amma na karshe da ta dauka shi ne a 1986 tare da Diego Maradona.
'Yan kwallon da suka buga wasanni da yawa a Gasar Kofin Duniya
Lothar Matthaus 25
Lionel Messi 24
Miroslav Klose 24
Paolo Maldini 23
Cristiano Ronaldo 21
Diego Maradona 21
Uwe Seeler 21
Wladyslaw Zmuda 21











