Asalin Covid-19: FBI ta ce da alama daga dakin bincike na China ta fito

Hoton shugaban FBI  Christopher Wray

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Shugaban hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka, FBI, Christopher Wray, ya ce hukumar ta yi amanna cewa bisa ga dukkan alamu cutar korona (Covid-19) ta samo asali ne daga wani dakin binciken kimiyya na gwamnatin China.

A hirarsa da kafar yada labarai ta FOX News, Mista Wray ya ce tun tsawon lokaci hukumar take nazari da ganin cewa asalin annobar mai yuwuwa ya fito ne daga dakin binciken kimiyya.

Wannan shi ne karon farko da hukumar ta FBI ta bayyana wannan bincike nata na sirri ga jama’a kan yadda annobar ta fara.

Masana kimiyya da dama sun nuna cewa babu wata sheda da ke nuna cewa cutar ta samo asali ne daga dakin kimiyya.

Haka kuma wasu hukumomin gwamnatin Amurkar sun fitar da sakamakon bincikensu ne wanda ya saba da na FBI.

Wasu daga cikinsu ko da yake ba tare da wani kwakkwaran tabbaci ba sun ce suna ganin kwayar cutar ta samo asali ne daga dabbobi zuwa mutane.

Ita dai Fadar Gwamnatin Amurka ta ce babu wata matsaya a tsakanin gwamnatin Amurka a kan asalin cutar.

Wani binciken hadin gwiwa da aka yi a 2021 na hukumar lafiya ta duniya da hukumomin China ya ce abu ne mawuyaci wannan zargi da ake yi na bullar cutar daga dakin kimiyya ya kasance haka.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Sai dai kuma binciken na hukumar lafiya ta duniya ya gamu da suka sosai, kuma tuni babban darektan hukumar ya nemi da a gudanar da sabon bincike, kuma ya ce nazarin a bude yake za a iya gudanar da karin bincike a kai.

Shugaban hukumar ta FBI, ya yi kalaman nasa ne na cewa bisa ga dukkan alamu cutar da bullo ne daga dakin gwajin kimiyya na China, kwana daya bayan jakadan Amurka a China ya bukaci kasar ta Sin da ta kasance mai gaskiya a kan bayyana asalin cutar.

A wannan tattaunawa da aka yi da shugaban, ranar Talata, Mista Wray ya ce China ta dage sosai wajen ganin ta dakile duk wani kokari na gano asalin annobar ta duniya.

A martanin da ta mayar game da zargin na FBI, gwamnatin China ta ce Amurka ta sa siyasa a cikin batun.

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen China Mao Ning ta ce matsayar da hukumar ta Amurka ta dauka ba ta da inganci da kimar da za a yi magana a kai.

Wasu nazarce-nazarcen da aka yi dangane da asalin annobar sun nuna cewa kwayar cutar ta yadu ne daga dabbobi zuwa mutane a birnin Wuhan na China, musamman ma daga kasuwarsu ta naman dabbobin dawa da na ruwa.

Kasuwar tana kusa da babban dakin binciken kimiyya ne wanda ya gudanar da nazari a kan kwayoyin cutar korona.

.

Asalin hoton, Google

A 'yan kwanakin da suka gabata , ma'aikatar makamashi ta Amurka ta ce ta gano da alama zargin da ake kwayar cutar ta samo asali ne daga dakin gwaji na kimiyya a Wuhan haka ne, to amma ba za ta ayyana hakan ba gaba-gadi.

A martanin da suka yi kan wannan magana, masana kimiyya da dama da suka yi nazari a kan asalin kwayar cutar sun ce ba wata sheda ta kimiyya da ke kara tabbatar da batun bullar cutar daga dakin kimiyya.

Farfesa David Robertson na Jami'ar Glasgow ya ce har yanzu suna ganin haka kawai cutar ta bulla kamar yadda kawayoyi kan yi, musamman daga wannan kasuwar naman dawa da halittun ruwa ta birnin Wuhan, amma ba waccan magana ta dakin kimiyya ba.

A ranar Litinin kakakin majalisar tsaro ta Amurka, John Kirby ya ce Shugaba Biden na goyon bayan duk wani kokari na gwamnati na gano asalin yadda cutar ta Covid-19 ta bullo.

Alaka tsakanin Amurka da China ta ta'azzara bayan batun bullar balan-balan din China a Amurka.

A makon nan wani kwamiti na jam'iyyun Amurkar biyu ya fara sauraren barazanar da jam'iyyar Kwaminisanci ta China ke yi ga Amurka.

Zaman farko na kwamitin musamman kan gogayya tsakanin Amurka da jam'iyyar Kwaminisanci ta China ya mayar da hankali ne kan batutuwan da suka hada da 'yancin dan'Adam da dogaron tattalin arzikin Amurka a kan masana'antun China.