Abin da ya kamata ku sani kan wasan Croatia da Brazil

Asalin hoton, Getty Images
Croatia da Brazil za su kara a wasan daf da na kusa da na karshe a Qasar Cin Kofin Duniya a Qatar ranar Juma'a a filin Educational City.
Croatia ta kawo wannan matakin bayan da ta yi ta biyu a rukuni na shida da maki biyar a rukunin da Morocco ta yi ta daya da ya hada da Belgium da kuma Canada.
Croatia, wadda ba ta taba lashe kofin duniya ba, wadda ta yi ra biyu a Rasha a 2018, ta yi nasara a kan Japan da ci 3-1 a bugun fenati a wasan zagaye na biyu, bayan da suka tashi 1-1 har minti na 120 ranar Litinin.
Ita kuwa Brazil ita ce ta daya a rukuni na bakwai da maki shida a rukunin da ya hada da Kamaru da Switzerland da kuma Serbia.
Brazil mai kofin duniya biyar ta doke Korea ta Kudu 4-1 a wasan zagaye na biyu ranar Lahadi.
Wasa na biyar da za su kara a tsakaninsu kuma na uku a Gasar Kofin Duniya, Brazil ta ci uku da canjaras daya a fafatawa hudun da suka yi a baya-
Na karshe da suka hadu a bayan nan shi ne a 2018 a wasan sada zumunta da Brazil ta yi nasara da cin 2-0.
Wasa bakwai daga takwas da Croatia ta yi a ziri daya kwale a babbar gasar tamaula sai an je karin lokaci da ita.
Ta kuma kai zagayen gaba sau hudu a kofin duniya - uku daga ciki a bugun fenariti a matakin kwaf daya.
To sai dai Croatia ta kasa cin tawaga daga Kudancin Amurka a fafatawa hudu daga biyar da ta yi, in banda doke Argentina 3-0 da ta yi a 2018 a Rasha.
Brazil wadda ta dauki kofin duniya a 2002 kuma na biyar, bayan doke Jamus 2-0 - tun daga lokacin ta kasa cin tawaga daga Turai a karawar ziri daya kwale a biyar da ta buga.
Wasannin da aka buga tsakanin Croatia da Brazil:
2017/2018
Wasan sada zumunta Ranar Lahadi 3 ga watan Yunin 2018
Brazil 2 - 0 Croatia
2013/2014
Gasar Kofin Duniya Ranar Alhamis 12 ga watan Yunin 2014
Brazil 3 - 1 Croatia
2005/2006
Gasar Kofin Duniya Ranar Talata 13 ga watan Yunin 2006
Brazil 1 - 0 Croatia
Wasan sada zumunta Ranar Laraba 17 ga watan Agustan 2005
Croatia 1 - 1 Brazil











