Real za ta yi wasa na 300 a Champions League a karawa da Liverpool

An wallafa

Real Madrid za ta karbi bakuncin Liverpool ranar Laraba a Champions League, wasa na 300 da za ta buga a gasar zakarun Turai kenan.

Real ce ta samu nasara a wasan farko da suka buga a bana a Anfield da cin 5-2 a zagayen 'yan 16 a Champions League.

Real Madrid mai kofi 14 ita ce kan gaba a lashe gasar tun da aka sauya fasalin wasannin a 1992/93, kuma ita ce kan gaba a yawan buga wasanni a gasar.

Wadda take ta biyu a yawan buga wasa a gasar ita ce Bayern Munich mai 280 da kuma Barcelona mai karawa 277 a Champions League.

Tun bayan da aka sauya fasalin gasar, Real ta dauki kofi takwas, sai Barcelona hudu, Bayern da uku da AC Milan mai uku, amma Real tana da 14 jmilla.

Ta fara daukar Champions League a 1998. a Amsterdam a wasa da Juventus, sannan ta kara dauka a 2000 a fafatawa da Valencia.

A shekarar 2002 ta kara lashe Champions League, bayan nasara a kan Bayern Leverkusen da ci 2-1.

A shekarar 2014 Real ta doke Atletico Madrid a Lisbon ta dauki kofin, sannan ta kara lashewa a Milan a 2016 a bugun fenariri da Atletico Madrid.

Real ce dai ta dauki Champions League a Kiev a 2018, bayan nasara a kan Liverpool da cin 3-1.

Haka kuma a bara Real Madrid ta ci Liverpool 1-0 a Paris ta dauki kofin Zakarun Turai.

Idan ka hada takwas da ta dauka bayan da aka sauya fasali daga 1992/93 da shidan da ta lashe a tsohuwar gasar zakarun Turai - kenan tana da 14 jimilla.