Man United ta dauki Martinez daga Ajax kan fam miliyan 57

Asalin hoton, Getty Images
Manchester United ta kammala daukar dan kwallon tawagar Argentina, mai tsaron baya Lisandro Martinez daga Ajax kan fam miliyan 57.
Kociyan United, Erik ten Hag ya yi murna da daukar dan kwallon mai shekara 24, wanda ya saya a lokacin yana horar da Ajax a 2019.
Ya koma Old Trafford kan kwantiragin kaka biyar da zai kare a karshen 2027 da yarjejeniyar za a iya tsawaitata zuwa kaka daya idan ya taka rawar gani.
Martinez ya yiwa Ajax wasa 120 tun bayan da ya koma Netherlands da taka leda daga kungiyar Argentina, Defensa y Justicia kan fam miliyan 6.3 a 2019, ya kuma taka leda a Newell's Old Boys.

Asalin hoton, Getty Images
Ya buga wa Argentina wasa bakwai tun lokacin da ya fara taka mata leda a Maris din 2019.
Ya kuma buga mata wasa a 2021 a gasar Copa America da kasar ta lashe a Brazil.
Martinez ya taka leda karkashin Ten Hag a Ajax ya kuma dauki Eredivisie a kungiya a 2021 da kuma 2022 da daukar Dutch Cup a 2021.
Shi ne kuma fitatcen dan wasan Ajax da ya taka rawar gani a kungiyar a kakar 2021-22.
Dan kwallon Argentina shi ne na uku da United ta saya a bana, bayan Christian Eriksen da Tyrell Malacia.
Haka kuma United tana ta kokarin daukar Frenkie de Jong daga Barcelona.










